An Shiga Matsin Lamba, Gwamnoni Sun Karbo Bashin N46.1bn Domin Biyan Albashi
- Wasu Gwamnoni sun rika karbo bashi daga bankuna saboda su biya ma’aikata albashi a jihohinsu
- Aron da gwamnatocin su ke karbowa ya jawo bashin da ke wuyan jihohin Najeriya ya karu a 2023
- Alkaluma sun nuna a yanzu bankuna uku ne aka fi maida hankali wajen karbo bashi daga gare su
Abuja - Wasu gwamnatocin jihohi sun karbo aron kusan N46.17bn daga bankuna uku tsakanin Janairu zuwa Yunin shekarar nan ta 2023.
Binciken Punch ya ce rahotonnin rabin shekara da aka samu daga bankunan Access, Fidelity da Zenith ya nuna jihohi sun karbo bashin kudi.
Gwamnonin kasar sun fi dogara ne da bankin Access wajen cin bashi a shekarar nan, inda a cikin watanni shida su ka ba jihohi aron N42.97bn.
Bankuna 3 sun taimaka da N46bn
Bankin Zenith ya bada aron N1.78bn sai jihohi su ka ci bashin N1.42bn daga bankin Fidelity.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya ce a cikin jihohi 36 da ake da su a kasar nan, ba a samu bayanai a kan jihohi irinsu Ribas, Sokoto, Akwa Ibom, Edo da Legas ba.
Sauran jihohin da babu bayanai game da kudinsu daga farkon shekarar bara zuwa bana su ne: Kaduna, Bauchi, Zamfara, Yobe da kuma Ogun.
Karancin kudin shiga a jihohi
Alkaluman da aka samu na jihohi 25 ya nuna gwamnonin sun yi harin samun N219.56bn a farkon 2023, amma a karshe N182.26bn aka iya samu.
Rahoton ya ce an samu gibin kusan 17% a hasashen kudin shigan da gwamnatocin jihohi su ka ci burin tatsa ta hanyar haraji a watannin farkon bana.
Bashin gwamnatocin jihohin Najeriya
Alkaluman da aka samu daga bankin CBN sun nuna bashin da bankunan kasuwa su ke bin jihohin nan ya karu zuwa N2.2tr a karshen watan Maris.
Kudin da ake bin jihohi a bankuna ya karu daga N1.97tr zuwa fiye da N2tr a cikin ‘yan watanni kadan, hakan ya na nufin bashi sun karu da N240bn.
Bayanan da aka samu daga ofishin DMO mai tattara bashi ya nuna jihohi 36 da Abuja sun karbo aron N5.8tr a gida da $4.35bn daga kasashen waje.
Gwamnati ta sasanta da NLC
Shugaban Kungiyar NLC ya ce ba su janye yajin aiki ba, sun dakata ne kurum na tsawon kwanaki 30 domin su ga gudun ruwan gwamnati.
Kwamred Joe Ajaero ya fayyace abin da ya hana ‘yan kungiyar NLC tafiya yajin-aikin da aka yi niyya, ya ce sun ji tausayin talakawan kasar ne.
Asali: Legit.ng