Shugaban Alkalai, Ariwoola Ya Gargadi Sabbin Alkalai Kan Cin Hanci
- Olukayode Ariwoola, shugaban alkalan Najeriya ya gargadi alkalai kan aiki tukuru ba tare da karbar cin hanci ba
- Ariwoola ya yi wannan gargadin ne yayin rantsar da sabbin alkalan babbar kotun Tarayya 23 a yau Laraba 4 ga watan Oktoba
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da yanke hukuncin zabe a kotu wanda a yanzu akwai jihohi da dama da ba a kammala ba
FCT, Abuja - Alkalin alkalan Najeriya, Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya gargadi sabbin alkalai da kada su saurari korafe-korafen jama'a.
Ya ce yayin yanke hukunci duk tasiri da girman korafin mutane kundin tsarin mulki ya fi shi.
Meye Ariwoola ya gargadi sabbin alkalan a kai?
Ariwoola ya bayyana haka ne a yau Laraba 4 ga watan Oktoba yayin rantsar da sabbin alkalai a Abuja.
Kungiyar NLC Ta Fadi Yawan Mafi Karancin Albashi Da Za Su Tattauna Da Gwamnati, Ta Yi Wa Ma'aikata Albishir
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bukaci alkalan da a kullum su rinka amfani da kundin tsarin mulki wurin yanke hukunci, Premium Times ta tattaro.
Ya kara da cewa ana yawan sukar alkalan Najeriya idan sun yanke hukunci, ya ce babu wani fahimta na mutane komai tasirinta da girmanta da zai fi karfin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya ce:
"Mafi yawan 'yan Najeriya sun dogara ne ga hukuncin da kotu za ta yanke.
"Saboda girman rantsuwa da kuka dauka yanzu, kun samu karin nauyi da kuma girma a rayuwa."
Ya bukaci alkalan da su yi aiki tukuru don ganin sun sauke nauyin da aka daura musu.
Ya kuma gargade su da karbar cin hanci da rashawa wanda ke rusa martabar kotu da alkalai, cewar Vanguard.
Wane martani jama'a su ka yi kan gargadin na Ariwoola?
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu 'yan Najeriya kan lamarin.
Salisu Adamu ya ce tabbas wannan gargadi ne mai jan hankali saboda Hausawa sun ce shari'a sabanin hankali.
Ya ce idan shari'a ba ta maka dadi ba, hakan ba ya na nuna an yi rashin adalci ba.
Wani da ya nemi a boye sunansa ya ce:
"Wannan alama ce ta cewa za su ci gaba da yanke hukunci yadda su ka ga dama a kotunan zabe."
Aliyu Muhammad ya ce babu abin da zai raba dan Najeriya musamman alkalai da cin hanci.
CJN Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalai
A wani labarin, Alkalin alkalan Najeriya, Mai Shari'a, Olukayode Ariwoola ya rantsar da sabbin alkalan kotun daukaka kara guda tara.
Rahotanni sun tabbatar cewa sabbin alkalan an rantsar da su ne a ranar 20 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng