Jami'ar Chicago: “Takardun Karatun Tinubu Ba Na Bogi Bane”, Inji Fadar Shugaban Kasa
- Fadar shugaban kasa ta yi karin haske dangane da sahihancin takardun karatun da Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa hukumar INEC
- Fadar shugaban kasa ta dage cewa takardun karatun da Tinubu ya gabatarwa INEC a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 ba na bogi bane
- Kakakin Tinubu, Temitope Ajayi, ya bayyana a ranar Laraba cewa babu kamshin gaskiya kan zargin da ake yi wa shugaban kasar na kirkirar takardun makaranta
Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin cewa an kirkiri takardun karatun da Shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a lokacin zaben shugaban kasa na 2023 ne.
Ku tuna cewa jami'ar jihar Chicago (CSU) ta saki takardun shaidar karatun Tinubu ga babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar a ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, bayan umurnin wata kotu.
Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, ya nemi a ba shi takardun domin marawa zarginsa kan takardun karatun Tinubu baya.
Magatakardar jami'ar ya ba da takardun shaidan karatun, amma an sami dan banbanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CSU: Fadar shugaban kasa ta yi martani ga ikirarin Atiku kan Tinubu a kotun Amurka
Da yake martani a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, kakakin Tinubu, Temitope Ajayi, ya bayyana cewa CSU ta tabbatar a rantsuwa cewa Tinubu ya halarci jami'ar kuma cewa makarantar ba ita ke kula da batun maye gurbin takardun da suka bata ba.
Ya ce babu kamshin gaskiya a ikirarin kirkirar takardun, yana mai cewa babu wanda zai iya kirkirar takardar da ya riga ya mallaka, rahoton Daily Trust.
Da ya garzaya shafinsa na X, Ajayi ya rubuta:
"Ya kamata mu fito fili.
Takardun Tinubu: Jigon PDP Ya Yamutsa Peter Obi Kan Kin Mika Takardar Digiri Ga INEC, Ya Nemi Bahasi
"A cikin bayanan da Jami’ar Jihar Chicago ta yi, babu inda Jami’ar ta ce takardar shaidar da Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC na bogi ne. Jami’ar ta nanata karkashin rantsuwa cewa shugaba Tinubu ya kammala karatunsa da karramawa, kuma duk da haka, yan kasuwa ne ke maye gurbin takardun shaidar kammala karatu da suka bata ba jami'ar ba.
"Ikirarin cewa Shugaban kasa Tinubu ya gabatar da takardun shaidar karatu na bogi ga INEC ba shi da ma'ana. Mutum ba zai iya kirkirar takardun karatu da ya mallaka ba. Kana iya kirkirar abun da baka da shi ne kawai."
Martanin yan Najeriya kan ikirarin kakakin shugaban kasa
Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a dandalin X dangane da jawabin Ajayi kan takardun karatu da Tinubu ya gabatarwa INEC.
@JeffreyGuterman ya yi martani:
"Ikiarrinka shirme ne tsantsa. Ka daina kare mai laifi."
@Ifenkeliya ce:
"Za ka yi bayani ka gaji babu hujja."
@josephanyaa ta ce:
"Lol. A wannan twitar, ba za ka iya siye mu dadin baki ba, kawai ka manta. kana iya uwa ga fada ma mutanen da ke kallon NTA duk shirmen da kake so, amma karairayinka ba zai karbu a wannan manhajar ba."
Jami’ar Amurka ta allaka masa takardun Tinubu, Atiku zai sheka kotun koli da karfinsa
A baya mun kawo cewa jami’ar jihar Chicago da ke kasar Amurka, ta damkawa Atiku Abubakar takardun karatun shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni daga Premium Times sun tabbatar da cewa lauyoyin ‘dan takaran shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar sun karbi takardun.
Asali: Legit.ng