Har Yanzu Babu Labarin ‘Dan Takaran Gwamna Shekaru 2 da Bacewarsa

Har Yanzu Babu Labarin ‘Dan Takaran Gwamna Shekaru 2 da Bacewarsa

  • Tun lokacin da aka dauke Obiora Agbasimalo a Satumban 2021, kusan babu wanda ya sake jin duriyarsa
  • Matar ‘dan takaran gwamnan ta shiga tsaka-mai-wuya , ta yi tsawon shekaru biyu ba tare da mijinta ba
  • Ana zargin Jam’iyyar LP ba ta taimakawa iyalan Obiora Agbasimalo sosai wajen gano inda ya shiha ba

Anambra - Shekara biyu kenan da bacewar Obiora Agbasimalo, a lokacin da ya fito neman takarar gwamnan jihar Anambra a karkashin LP.

Premium Times ta tuno da yadda Mista Obiora Agbasimalo ya bace a ranar 18 ga watan Satumba 2021, har yau ba ayi nasarar kubutar da shi ba.

Kafin ya shiga takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta LP, ‘dan siyasar ya yi shekaru kusan 15 ya na aiki a banki, sai ya burma a harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Maida Ma'aikata Sama da 700 da Gwamnati Ta Kora Daga Aiki, Zai Biyasu Albashi Tun 2018

'Dan takaran gwamnan Anambra
Obiora Agbasimalo mai takaran gwamna a LP Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Lokacin da aka sace Obiora Agbasimalo

An yi awon gaba da Agbasimalo ne a kauyen Lilu da ke karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra a lokacin ya na yawon kamfe a yankin Azhia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lokacin da abin ya auku, ‘dan takaran ya na tare da jami’an ‘yan sandan da ke gadin tawagarsa, sa’ilin wata guda ya rage a shirya zaben gwamna.

An bar mai dakin Agbasimalo da jimami

Rahoton ya ce mai dakin ‘dan takaran, Eucharia Agbasimalo, ta gigice da samun labarin sace sahibinta, amma ta na mai sa ran sake ganin shi.

Sakataren LP na kasa, Clement Ojukwu ya yi wa Eucharia Agbasimalo alkawarin mijinta zai dawo, har yau ba ta sake ido daya da masoyinta ba.

Jam’iyyarsa ta LP ta cigaba da yawon kamfe, ta na mai cewa za a fito da Agbasimalo bayan zabe. Jaridar Sahara Reporters ta fitar da rajoton nan.

Kara karanta wannan

Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi Ana Kokarin Tantance Sababbin Ministoci a Majalisa

Labarin 'dan takaran LP ya canza

Wata da watanni da yin zaben, har an rantsar da sabon gwamna tun 2021, amma babu labarin wanda ake nema, hakan ya tada hankalin jama'a.

Da farko jagororin jam’iyyar adawar sun rika nuna wadanda su ka yi garkuwa da ‘dan takaran gwamnan, su na bada dama mutane su yi magana da shi.

Shugaban LP na kasa, Julius Abure ya fadawa iyalin wanda aka sace cewa sun sanar da ‘yan sanda da jami’an SSS game da abubuwan da su ka faru.

Yayin da mai dakinsa ta ziyarci ofishin SSS, sai ta fahimci cewa Abure bai ankarar da jami’an tsaro ba, ya sanar da su labarin ne sai ya yi gaba kurum.

Binciken Diezani Alison-Madueke

Ku na da labari tun da tsohuwar ministar ta bar gwamnatin tarayya a 2015 ake wasan kura da ita a gida da ketare saboda zargin sata da cin amana.

Kara karanta wannan

Rigima: Mataimakin Gwamnan PDP Ya Bar Gidan Gwamnati Ya Koma Sabon Ofishinsa, Ya Roƙi Allah

Alkalin wani kotun da ke Birtaniya, Michael Snow ya bada belin Diezani Alison-Madueke a kan £100,000, alhali EFCC na neman ta cafko daga waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng