Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Karin Ministoci Uku a Majalisar Shugaba Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Karin Ministoci Uku a Majalisar Shugaba Tinubu

  • Majalisar dattawa ta yi nasarar tantance karin zababbun ministoci uku da Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada
  • Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, ya tabbatar da Balarabe Abbas Lawal, Dr Jamila Bio Ibrahim da Mista Ayodele Olawande a ranar Laraba
  • A watan Agustan 2023 ne majalisar ta tantance tare da tabbatar da zababbun ministoci 45 tare da kin amincewa da wasu uku

Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta sake tabbatar da karin ministoci uku a kan guda 45 da ta amince da su a watan Agusta.

Ministocin da majalisar ta tabbatar da su a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba sun hada da Jamila Bio Ibrahim daga jihar Kwara; Balarabe Lawal daga jihar Kaduna; da Ayodele Olawande daga jihar Ondo.

Majalisar dattawa ta tabbatar da zababbun ministoci uku
Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Karin Ministoci Uku a Majalisar Shugaba Tinubu Hoto: Jounalist KC
Asali: Facebook

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya aike wasika zuwa majalisar dattawan, inda ya nemi ta tabbatar da zababbun ministocin nasa, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Wakilin Jihar Kaduna Ya Fadi Ana Kokarin Tantance Sababbin Ministoci a Majalisa

An nada Dr. Ibrahaim da Mista Olawande a matsayin ministar matasa da kuma karamin ministan matasa, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kimanin awanni biyu da rabi da fara shirin, wanda aka fara da misalin karfe 1:00 na rana, shugaban majalisar dattawa, Godwill Akpabio, ya gabatar da zaben wadanda aka nada.

Sanatocin sun kada kuri'unsu inda suka tabbatar da zababbun ministocin.

Da farko, an sha yar dirama a zauren majalisar, inda Lawal ya yanke jiki ya fadi bayan ya gama gabatar da kansa, lamarin da yasa mutane da dama da ke wajen garzayawa inda yake don basa taimakon gaggawa.

Koda dai wakilin na jihar Kaduna bai samu amsa tambayoyi ba saboda faruwar lamarin, majalisar ta tabbatar da shi. Sannan ya farfado bayan dan kankanin lokaci.

Jama'a sun yi martani

Kamar yadda aka saba bisa al'ada, yan Najeriya sun garzaya sashin sharhi na Channels TV a dandalin X don tofa albarkacin bakunansu kan lamarin.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Majalisa Ta Fara Tantance Balarabe Da Sauran Mutane 2 Da Tinubu Zai Nada Minista

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@adaobiotu ya rubuta:

"Sun kuma tabbatar da mutumin da ya yanke jiki ya fadi a yayin shirin tantancewar? Wow!"

@stephen_ogugua ta rubuta:

"Kuma mutane na son kasar nan ta yi aiki? Mutum ya fadi sannan ya tsallake tantancewar?"

@akwaibomdaily ya rubuta:

"Na taya ku murna."

Wakilin jihar Kaduna ya fadi a wajen tantance ministoci

A baya Legit Hausa ta kawo cewa Balarabe Abbas Lawal ya fadi kasa a yayin da ake tantance karin ministocin tarayya.

Malam Balarabe Abbas Lawal ya na cikin wadanda mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da sunayensu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng