Bidiyon Wani Mutum Da Yar Wada a Otel Ya Yadu, Jama’a Sun Yi Cece-Kuce
- An gano wata yar wada tare da wani mutum a cikin otel, kuma bidiyonsu ya yadu a soshiyal midiya
- A cikin dan gajeren bidiyon, an gano wata ma'aikaciyar otel din tana kula da mutumin da yar wadar
- Bayan sun kammala daga wajen tarban baki na otel din, sai suka garaya ciki, lamarin da yasa mutane hasashen abubuwa da dama
Masu amfani da dandalin soshiyal midiya sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum a cikin otel tare da wata yar wada.
Enigma ne ya fara yada dan gajeren bidiyon amma dai bai bayyana a ina ne aka dauki bidiyon ba.
Matashi da yar wada sun shiga otel
A cikin bidiyon, an gano yar wadar da mutumin tare da wata matashiya da ake tunanin mai tarban mutane ne a otel din ce.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayan mai tarban mutanen tkammala da su, sai suka garzaya saman otel din a tare.
Mutane da dama sun yi martani a kan bidiyon inda wasu suka cika d mamakin dalilin yada shi a soshiyal midiya.
Kalli bidiyon a kasa:
Masu amfani da Twitter sun yi martani kan bidiyon wani mutum da wada a otel
Mutanen soshiyal midiya sun yi hasashe daban-daban kan abun da ke gudana a bidiyon.
@iamthepreence ya ce:
"Babu wani abu mai kama da sirri kuma a yanar gizo...wasunmu basu da karfin kallon irin wadannan bidiyon. Don Allah ka sauke shi sannan ka saka cikakken bidiyon."
@KanuArnold ya tambaya:
"Me yasa wannan ya yi kama da abun dariya a wajena? Abubuwa da dama na yawo a kwanya na."
@TonyChinaza ya ce:
"Manta cewa yarinyar nan tana da gajarta fa, amma tana da abun da dukkan maza ke bukata a mace wanda shine kugu."
@Wildorah ta ce:
"Manya biyu suna rayuwarsu, kwatsam! Sai ka fito da wayarka ka fara yi masu bidiyo, saboda wani dalili?"
Matashiya ta nunawa duniya masoyinta dan tsurut
A wani labarin kuma, wasu masoya sun tashi kan jama'a a soshiyal midiya bayan sun baje kolin soyayyarsu.
An dai gano matashiyar dauke da sahibinta wanda ke dan kankantar jiki lamarin da ya dauki hankalin mutane da dama.
Asali: Legit.ng