Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazana Ga Shettima, Gawuna da Alkalai a Bidiyo

Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazana Ga Shettima, Gawuna da Alkalai a Bidiyo

  • Jami'an DSS sun cafke matashiyar nan da ta yi barazanar halaka Shettima, Gawuna da Alƙalan Ƙotun Kano kuma ta kashe kanta
  • Fiddausi Ahmadu, 'yar kimanin shekara 23 a duniya ta yi wannan barazana ne a wani faifan bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya
  • Ta ce duk inda ta ga Gawuna ko shugabar alƙalan da suka kwace nasarar NNPP zata iya tashin bam kowa ya mutu

Jihar Kano - Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta damƙe matar da ake zargin ta yi barazanar kashe kanta kuma ta kashe duk mai hannu a nasarar da APC ta samu a Kotun zaɓen gwamnan Kano.

Matar mai suna Fiddausi Ahmadu, ta yi barazanar cewa zata yi ƙunar baƙin wake ta kashe duk wanda ya taimaka ɗan takarar APC, Nasiru Gawuna, ya samu nasara a Kotu, sannan ta kashe kanta.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Wanda Ya Lashe Zaben Gwamnan Jihar Adamawa

Jami'an hukumar tsaron farin kaya DSS.
Kano: DSS Ta Kama Matar da Ta Yi Barazana Ga Shettima, Gawuna da Alkalai a Bidiyo Hoto: DSS
Asali: Twitter

Leadership ta tattaro cewa idan baku manta ba, Kotun sauraron ƙararrakin zabe ta ayyana Gawuna a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano bayan soke wasu ƙuri'u.

A rahoton da muka kawo muku, Kotun ta umarci INEC ta janye Satifiket ɗin da ta bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP, kana ta bai wa Gawuna sabon shaidar cin zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Su wa matashiyar ta yi wa barazana?

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, matashiyar yar shekara 23 a duniya ta yi iƙirarin cewa zata yi yaƙin kwato haƙƙin NNPP da Gwamna Abba Gida-Gida.

A faifan bidiyon, an ji Fiddausi a harshen Hausa Hausa tana barazana ga shugabar kotun, inda ta yi gargadin cewa duk inda ta ga Alkalin, ita (Fiddausi) ba za ta damu ba ta tashi bam su mutu baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Har ila yau, Fiddausi ta gargadi Gawuna, tana mai cewa, "Kada ka kuskura na gano inda kake, zan ɗaura Bam da ni da kai mu mutu baki ɗaya ba."

Ta kuma caccaki mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Ƙashim Shettima, inda ta kira shi da sunaye daban-daban tana zarginsa da kitsa manaƙisar raba NNPP da mulkin Kano.

A cewarta, idan da za a tara mata Ganduje, Gawuna, Rarara da Alkalan da suka yanke hukunci a wuri ɗaya, zata iya shiga da Bam ta tashe su baki ɗaya, Daily Post ta rahoto.

"Zamu gurfanar da Fiddausi a gabam Ƙuliya saboda bai kamata a kauda ido a ɗauki wannan barazana da wasa ba," inji wata majiya daga hukumar DSS.

'Yan Bindiga Sun Shiga Jami'ar Usman Ɗanfodio Da Ke Jihar Sakkwato

A wani rahoton kuma Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun kai farmaki jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke jihar Sakkwato ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Jami'an Tsaro Zasu Kama Kwankwaso Kan Barazana Ga Rayuwar Alkalan Kotu? Sabbin Bayanai Sun Fito

Maharan sun kutsa kai cikin ƙaramar kasuwar makaranatar wacce ake kira, 'Mini Market' inda suka kwashi kayayyaki da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262