Jerin Tallafin Shugaba Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur

Jerin Tallafin Shugaba Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu damar kulla yarjejeniya da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago bayan wani taro da suka yi a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba a fadar shugaban ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin fara yajin aiki na bai-ɗaya a faɗin ƙasar nan, wanda ƙungiyoyin ƙwadago suka shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.

Gwamnatin Tinubu ta yi karin albashi
Gwamnatin Tinubu ta sanar da karin albashi ga ma'aikata Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cewar sanarwar da Mallam Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ya fitar, Shugaba Tinubu, wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan fadarsa, Femi Gbajabiamila, ya cimma matsaya da shugabannin.

Wasu daga cikin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma sun haɗa da:

1. Ƙarin albashi

Bayan taron, gwamnatin tarayya ta sanar da ƙarin albashin wucin gadi na N25,000 ga duk ma'aikatan gwamnatin tarayya da take biya daga asusunta na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Sake Yin Wata Hubbasa 1 Domin Hana NLC Shiga Yajin Aiki Ranar Talata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Legit.ng ta rahoto, ƙarin N25,000 za a yi ne ga ƙananan ma'aikatan gwamnati.

A halin da ake ciki kuma, Dada Olusegun, mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, ya tabbatar da cewa ƙarin albashin wucin gadi na Naira 35,000 na duk ma'aikatan gwamnatin tarayya ne kuma zai ɗauki tsawon watanni shida.

2. Gyaran Sufuri

Kamar yadda sanarwar ma’aikatar yada labarai ta tarayya da wayar da kan jama’a ta kasa ta fitar, an cimma matsaya kan gaggauta samar da motocin bas ɗin da za su riƙa amfani da iskar gas (CNG).

Ana sa ran wannan sabon shiri zai sauƙaƙa matsalolin sufurin da jama'a ke fuskanta waɗanda ke da alaƙa da cire tallafin man fetur.

Gwamnatin tarayya ta ce za a aiwatar da shirin a duk faɗin ƙasar nan.

3. Kuɗaɗe don ƙananan ƴan kasuwa

Kara karanta wannan

Diyyar N30bn: Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotu, Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka

Domin samun dorewar tattalin arziki da dogaro da kai ga ƴan kasa, gwamnatin tarayya ta kuma amince ta tallafawa masu ƙananan sana’o’i.

Duk da cewa har yanzu ba a bayyana adadin kuɗaɗen da aka ware domin gudanar da wannan shiri ba, ana sa ran za a aiwatar da shi a duk faɗin ƙasar nan.

4. Cire harajin VAT kan man dizal

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa za a rage harajin VAT ga ƴan ƙasar da ke amfani da man dizal domin motocinsu da samar da wutar lantarki.

A cewar sanarwar, cire harajin zai kasance na tsawon watanni shida.

5. Bayar da alawus na wata-wata ga iyalai miliyan 15

Hakazalika, gwamnatin tarayya ta cimma matsaya mai muhimmanci da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago ta hanyar sanar da biyan N75,000 ga gidaje miliyan 15.

Waɗannan gidaje za su karɓi N25,000 a kowanne wata har na tsawon watanni uku, daga Oktoba zuwa Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ƙungiyoyin Kwadago Sun Yi Fatali da Taron Da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya A Villa

Gwamnati Ta Shawo Kan Ma'aikata

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta samu damar cimma yarjejeniya da ma'aikata domin hana su shiga yajin aikin da suka kuɗiri aniyar farawa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta cimma matsaya da ƙungiyoyin ƙwadago domin fasa shiga yajin aikin sai baba-ta-gani da suka yi niyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng