Tinubu Ya Sanar Da Karin Albashi Ga Dukkan Ma’aikata Bayan Ganawar FG Da Kungiyar Kwadago

Tinubu Ya Sanar Da Karin Albashi Ga Dukkan Ma’aikata Bayan Ganawar FG Da Kungiyar Kwadago

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta amince da yi wa ma'aikata gaba daya karin albashin N35,000 na tsawon watanni shida
  • Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan a yammacin ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba
  • FG ta dauki wannan matakin ne a kokarinta na ganin kungiyar kwadago bata shiga yajin aikin da take shirin farawa a ranar Talata ba

Fadar shugaban kasa, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da karin albashin wucin gadi na N25,000 ga ma'aikata a dukkan matakai.

Kamar yadda NTA News ta rahoto, Shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ne ya sanar da hakan bayan ganawar da gwamnatin tarayya ta yi da shugabannin kungiyar kwadago.

Gwamnatin tarayya ta amince da lkarin albashin ma'aikata baki daya
Tinubu Ya Sanar Da Karin Albashi Ga Dukkan Ma’aikata Bayan Ganawar FG Da Kungiyar Kwadago Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Da yake magana a karshen taron, Gbajabiamila, ya bayyana cewa shugabannin kungiyar kwadago (NLC), da na kungiyar kasuwanci (TUC) sun cimma wasu matsaya tare da gwamnatin tarayya, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

NLC Da TUC Sun Janye Tafiya Yajin Aikin Gama Gari Na Tsawon Kwanaki 30 Bayan Ganawa Da FG

A yammacin ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba ne dai gwamnatin tarayya da kungiyar kwadagon suka shiga ganawar, a wani yunkuri na hana su shiga yajin aikin sai baba ta gani da suke shirin tafiya daga ranar Talata, 3 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da farko shugaban kasar ya sanar da cewar karin albashin wucin gadi na N25,000 da za a yi ga kananan ma'aikatan tarayya.

Tanadin da gwamnatin tarayya ta yi kan illar cire tallafin mai

A cikin wata sanarwa da ya fitar a karshen taron, ministan labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta jajirce wajen ganin an gaggauta shigo da motocin bas masu amfani da gas don saukaka wahalar sufuri sakamakon cire tallafin man fetur.

Ya kara da cewar gwamnatin tarayya za ta samar da kudade ga masu kananan sana’o’i, yana mai cewa za a cire haraji kan man diesel na watanni shida masu zuwa.

Kara karanta wannan

Babu Wata Yarjejeniya Da Emefiele Kan Dawo da ‘Biliyan 50’, Gwamnatin Tinubu

Sanarwar ta ce:

"Gwamnatin tarayya za ta fara biyan N75,000 ga iyalai miliyan 15 kan N25,000 duk wata, na tsawon watanni uku daga watan Oktoba zuwa Disamban 2023.”
“Za a kafa wani karamin kwamiti da zai yi aiki kan cikakkun bayanan aiwatar da duk wasu abubuwa don yin la’akari da su dangane da kokarin gwamnati na dakile illar cire tallafin mai.
“NLC da TUC za su yi la’akari da tayin da gwamnatin tarayya ta yi da nufin dakatar da yajin aikin da suka shirya domin samun damar tuntubar juna kan aiwatar da kudurorin da ke sama.”

Legit Hausa ta tattauna da wata ma'aikaciyar gwamnati don jin yadda ta dauki batun karin albashi da gwamnatin tarayya ke shirin yi.

Malama Sa'adatu Sha'aba ta ce tana fatan gwamnatin tarayya ta cika wadannan alkawara da ta dauka a wannan karo domin dai sun gaji da gafarar sa babu kaho.

Sa'adatu ta ce:

"Ai idan dai irin wannan alkawara ne mun saba ji, a kullun gwamnati ta ga da gaske ake za a dauki mataki sai ta kirkiro wasu alkawara na wucin gadi wanda yawanci ma ba aiwatar da su ake yi ba.

Kara karanta wannan

Karin Albashin N35k Da Jerin Tallafin Da Shugaba Tinubu Ya Fito Da Su Bayan Cire Tallafin Man Fetur

"Muna dai fatan wannan gwamnati ta shugaban kasa Bola Tinubu ba za ta yi mana irin kanzon kuregen da aka saba mana a baya ba. Ki duba fa yanzu sam albashin ma babu wani albarka tun kafin ya shigo an gama cinye shi. Amma kullun jiya iyau.

Yan Najeriya sun koka yayin da farashin gas ya doshi N1000

A wani labarin, mun ji cewa yan Najeriya sun nuna rashin jin dadi da tashin farashin gas din girki, wanda aka ce ya kai kimanin N1,000 kan kowace kg.

Wadanda suka siya gas a baya-bayan nan sun fada ma jaridar Legit cewa basu ji dadin karin kudin gas da aka yi ba da yadda ake ci gaba da wahala a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel