Kotun Ogun Ta Tabbatar da Zaben Gwamna Abiodun Na APC, Ta Kori Karar Adebutu Na PDP
- Kotu ta tabbatar da zaben gwamna Dapo Abidion a karo na biyu a zaben 2023 bayan zaman shari'ar na tsawon lokaci
- An bayyana koran karar da PDP da dan takararta na gwamna suka shigar don kalubalantar zaben da aka gudanar a bana
- Ana ci gaba da kakkabewa da tabbatarwa game da kararrakin da aka shigar kan zabukan bana a Najeriya
Jihar Ogun - Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Ogun ta bayyana Gwamna Dapo Abiodun, dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris, Channels Tv ta ruwaito.
Jam’iyyar PDP da dan takararta na gwamna, Ladi Adebutu sun kalubalanci sake zaben Abiodun kan zargin cin hanci da rashawa da rashin bin ka’idojin doka a zaben bana.
Karar ta kuma ce gwamnan bai samu rinjayen kuri’un da har INEC za ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben ba.
Hukuncin da kotu ta yanke
Da take zartar da hukuncin a ranar Asabar a zaman da aka kwashe kusan awanni 11 ana yi, kotun ta ce PDP ta gaza tabbatar da hujjoji kan abin da take zargi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, kotun ta bayyana yin watsi da karar tare da korar korar a gabanta, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Kotun ta kuma bayyana cewa Abiodun ya cancanci tsayawa takara a jam’iyyarsa kana ya cancanci ayyanawar INEC a zaben na bana.
Halin da ake ciki a jihar Ogun
Ya zuwa yanzu, an jibge jami'an tsaro don tabbatar da bin doka da oda a inda aka yanke hukuncin.
Kotunan kararrakin zabe a Najeriya na ci gaba da yanke hukunci kan kararrakin da aka shigar bayan kammala zaben bana.
Hakazalika, yanzu dai ba a bayyana ko yanke hukuncin ya kai ga fara murna ko korafi daga mazauna jihar ba.
Yadda aka kaya a kotun zaben jihar Kaduna
A wani labarin, an yanke hukuncin zaben gwamnan jihar Kaduna kamar yadda aka yi a sauran jihohi.
Kamar jihar Kano, kotun da ke Kaduna ta yanke shawarar gabatar da shari'ar ta manhajar 'Zoom'.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Isa Ashiru na kalubalantar zaben Gwamna Uba Sani na jam'iyyar APC da aka gudanar a watan Maris, Daily Trust ta tattaro.
Asali: Legit.ng