Inuwar Lema Ta Yi Dumi, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Lallaba Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Inuwar Lema Ta Yi Dumi, Tsohon Gwamnan Kaduna Ya Lallaba Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

  • Rahoton da muke samu ya bayyana yadda jigon PDP kuma tsohon gwmanan jihar Kaduna ya bar jam'iyyarsa
  • Ya tura wasika ga shugaban PDP tare da mika katin shaidar zama dan jam'iyyar PDP duk da ya jima a cikinta
  • Ba sabon abu bane dan siyasa ya tsalle daga jam'iyya zuwa wata jam'iyya ba, hakan na yawan faruwa a Najeriya

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Muktar Ramalan Yero, ya lallaba tare da raba gari da jam’iyyar PDP.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Satumba da tsohon gwamnan ya sanya wa hannu, Daily Trust ta ruwaito.

Rahoto ya bayyana cewa, ya aika wa shugaban jam’iyyar PDP Kaura na karamar hukumar Zaria ta jihar ne wannan wasikar.

Kara karanta wannan

Mafita: Jigon APC ya ba da shawarwari 5 ga Tinubu don magance aukuwar yajin aiki

Ramadan Yero ya fice daga PDP
Tsohon gwamnan Kaduna ya fice daga PDP | Hoto: Ramalan Yero
Asali: Twitter

Sakon Yero ga PDP

Abin da tsohon gwamnan ya fadi a cikin wasukar shi ne:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Tare da godiya ga Allah Madaukakin Sarki, na rubuto wannan wasikar ne don mika sakon gaisuwata tare da sanar da ku shawarar da na yanke na ficewa daga jam’iyyar PDP.
“Saboda haka, ina mai mika takardar murabus a matsayin dan jam’iyyar APC daga ranar 30 ga watan Satumba, 2023. Tare da wasukar, akwai katin zama dan jam’iyyata a hade."

Waye Yero a jihar Kaduna?

Yero, wanda kuma shi ne Dallatun Zazzau, ya taba zama mataimakin gwamna ga marigayi Gwamna Patrick Yakowa wanda ya mutu a hatsarin jirgin sama.

Daga nan ya zama Gwamnan Jihar Kaduna tsakanin 15 ga Disamba 2012 zuwa 29 ga Mayu, 2015.

Ya zuwa yanzu, ba a dai ji dalili daga tushe na abin da ya kai ga wannan fitaccen jigo na PDP ya fice daga jam'iyyar ba.

Kara karanta wannan

Uba Sani: Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Kan Hukuncin da Kotu Zabe Ta Yanke a Jihar Kaduna

Tsohon minista ya bar PDP

A wani labarin, tsohon ministan ayyuka a Najeriya kuma babban jigon jam'iyyar PDP, Chief Mike Oziegbe Onolememen, ya yi murabus daga kasancewarsa mamban jam'iyyar.

Onolememen ya tabbatar da fice wa daga jam'iyyar PDP a wasika mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba, 2023, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.

Tsohon ministan ya bayyana cewa ya yanke shawarin barin jam'iyyar PDP ne saboda yawan rigingimun cikin gida da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.