Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Masu Bauta Da Ke Hanyar Tafiya a Ondo
- Yan bindiga sun yi garkuwa da akalla masu bauta ashirin da biyar da ke hanyar tafiya a hanyar Ifon da ke karamar hukumar Ose ta jihar Ondo
- Mutanen da aka sace sun kasance mambobin cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Igan a Akure, babban birnin jihar
- Maharan sun sace matafiyan yayin da suke hanyar zuwa wani taron binne gawa a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba
Jihar Ondo - Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mambobin cocin Christ Apostolic Church (CAC), Oke Igan a Akure, babban birnin jihar.
An farmaki masu bautan ne a hanyar Ifon da ke karamar hukumar Ose ta jihar yayin da suke hanyar zuwa wani taron jana'iza a ranar Juma;a, 29 ga watan Satumba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Yan bindiga sun yi garkuwa da masu bauta 25
Wani mamba na cocin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai kuma ya ce yawancin masu bautan sun kasance mawakan coci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Akalla mutum ashirin da biyar ne a cikin motar bas din da ke tafiya zuwa wajen wani taron jana'iza a hanyar karamar hukumar Ose. Yan bindiga sun sace su sannan aka yasar da motarsu a bakin hanya."
Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace mutanen
Kakakin yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ya ce an tura rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane da sauran tawagar tsaro zuwa cikin jeji don ceto mutanen da aka sace.
"Amma tuni muka fara bibiyar masu garkuwa da mutanen da nufin ceto wadanda aka sace. Jami'anmu daga sashin yaki da garkuwa da mutane suna kakkabe jeji."
'Yan bindiga sun yi awon gaba da masu gudanar da bauta a jihar Kaduna
A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa, yan ta'addan da suka dira a coci a ƙaramar Chikun ta jihar Kaduna, sun yi awon gaba da masu bauta mutum 40.
Shugaban hukumar kiristoci ta Najeriya (CAN), reshen jihar Kaduna, Rev Joseph John Hayab, ya bayyana cewa mutum 15 daga cikin waɗanda aka sacen sun dawo wajen iyalan su, cewar rahoton Vanguard.
A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Kiristoci (CAN) ta jihar Kaduna, ya rabawa manema labarai a jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng