Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Kaurace Wa Taron Da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya
- Wakilan ƙungiyoyin NLC da TUC sun yi watsi da taron da gwamnatin tarayya ta shirya a fadar shugaban ƙasa ranar Jumu'a
- Ministan kwadago da shugaban ma'aikatan Villa sun kammala shirin taron amma shiru shugabannin ƙungiyoyin suka ƙi zuwa
- Wata majiya ta tabbatar da cewa an ɗage zaman zuwa ƙarshen makon nan amma ba ta san ainihin ranar da aka sa ba
FCT Abuja - Kungiyar Kwadago ta yi watsi da taron da gwamnatin tarayya ta shirya a wani bangare na kokarin dakile yajin aikin da ma’aikata ke shirin fara wa faɗin a Najeriya.
Daily Trust ta rahoto cewa shugaban ma'aikatan shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da Ministan kwadago da samar da aiki, Simon Lalong, sun kira taron a Villa.
Wakilan gwamnatin tarayya sun tsara zama da shugabannin ƙungiyoyin kwadago na ƙasa da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Jumu'a a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Diyyar N30bn: Gwamnatin Jihar Kano Ta Yi Martani Kan Hukuncin Kotu, Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka
Amma taron bai gudana ba saboda bangaren ƙungiyoyin kwadagon ba su halarci wurin da aka tsara yin zaman ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hangi Lalong a ofishin shugaban ma’aikata suna shirye-shiryen taron, amma har zuwa karfe 5:30 na yamma ba a ga shugabannin NLC da TUC ba su hallara ba.
Duk wani yunƙurin jin dalilan da ya sa ƙungiyoyin suka ƙaurace wa zaman jiya da daddare ya ci tura, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
An ɗaga zaman zuwa ƙarshen mako
Majiya da ke kusa da ofishin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ta ce an dage zaman ne zuwa karshen mako, inda ya ce bai san ainihin ranar da aka maida taron ba.
Ya ce:
"Duk sun tafi kowa ya kama gabansa tunda wakilan NLC da TUC ba su zo ba. Tabbas akwai dalili kuma na yi imani da cewa sun bayyana dalilansu ga wadanda ke jiransu."
"Na fahimci cewa sun ɗaga taron zuwa wani lokaci a ƙarshen makon nan, amma ban san ranar da suka sanya ba."
Ƙungiyoyin ma'aikatan Najeriya sun bada sanarwan cewa zasu dakatar da komai, su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 3 ga watan Oktoba, 2023.
Shugaba Tinubu Ya Dawo Najeriya
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya ranar Jumu'a da daddare mako ɗaya bayan kammala taron UGGA a ƙasar Amurka.
Ba bu wanda ya san inda shugaban ƙasar ya wuce bayan taron kuma rahoto ya nuna ya baro New York tun 22 ga watan Satumba, 2023.
Asali: Legit.ng