Yadda Wasu Matasa Suka Lakadawa Murja Kunya Dukan Tsiya a Kano

Yadda Wasu Matasa Suka Lakadawa Murja Kunya Dukan Tsiya a Kano

  • Wasu matasa da ba a san ko su waye ba sun lakadawa jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, mugun duka
  • Matasan wadanda ba a san dalilinsu na dukan jarumar ba sun ji mata raunuka a fuska inda suka sauya mata kamanni
  • An yi kira ga jami'an tsaro da su kwatowa jaruma Murja hakkinta ta hanyar gurfanar da wadanda suka yi mata aika-aikar

Jihar Kano - Rahotanni sun kawo cewa wasu tsagerun mutane da ba a san ko wanene ba sun lakadawa fitacciyar jarumar nan mai barkwanci a TikTok, Murja Ibrahim Kunya, dukan tsiya.

Kamar yadda jaridar Leadership Hausa ta rahoto, lamarin ya afku ne a cikin garin Kano a yammacin ranar Alhamis.

Matasa sun yi wa Murja kunya dukan tsiya
Yadda Wasu Matasa Suka Lakadawa Murja Kunya Dukan Tsiya a Kano Hoto: Murja Ibrahim Kunya
Asali: TikTok

Yadda matasa suka yi wa Murja Kunya dukan kawo wuka

Tuni hotunan lamarin ya yadu a shafukan soshiyal midiya inda aka gano yadda matasan suka ji wa jarumar raunuka a fuska tare da sauya mata kamanni.

Kara karanta wannan

“Ba Zai Ci Amana Ba”: Budurwa Yar Najeriya Ta Yi Caraf Da Masoyinta Da Tsurut Kamar Karamin Yaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, har yanzu ba a san ainahin dalilin da yasa suka aikata mata hakan ba.

Abokan huldarta da dama musamman yan uwanta yan TikTok sun fito sun yi Allah wadai da wannan abu da aka yi wa abokiyar tasu.

Harma wasu sun yi kira ga jami'an tsaro da su bi mata hakkinta ta hanyar kamo wadanda suka aikata mata wannan ta'asar tare da hukunta su a gaban doka.

Murja Kunya ta yi fice sosai a duniyar TikTok inda take nishadantar da mutane ta hanyar sakin bidiyoyi masu ban dariya kuma tana da tarin mabiya a shafin nata.

Ta kuma kasance yar fafatukar siyasa wacce ke goyon bayan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wato Abba Gida-Gida.

Hakan yasa har ya sanya ta cikin jerin wadanda zai aurar a shirin gwamnatinsa na aurar da zaurawa.

Kara karanta wannan

Yadda aka kamo wasu mutum 5 da suka yunkurin siyar da jariri mai kwanaki 8 a Kano

Tsakanin hukumar Hisban jihar Kano da matasa yan TikTok

A wani labarin, mun kawo a baya cewa an samu balahira tsakanin ƴan TikTok da kuma hukumar hisba dake rajin ganin an samu tarbiyya irin ta addinin musulunci a jihar Kano.

Hakan tasa da yawa daga cikin su suka baƙunci bayan kanta, gidan cin gabza da gidan gyaran hali. A yayin da wasu suka sha bulala, da kuma tara haɗi da horon shara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng