Gwamnatin Tarayya Ta Gayyaci NLC Da TUC Zuwa Taron Gaggawa a Abuja
- Gwamnatin tarayya ta shirya taron gaggawa da jagororin kungiyoyin kwadago a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja
- Wannan dai wani yunkuri ne na daƙile shirin NLC da TUC na tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 3 ga watan Oktoba
- Tuni saƙon gayyata zuwa taron ya riski ƙungiyoyin amma gwamnati ta ƙara lokaci domin ba su damar kiran masu ruwa da tsaki
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta kira taron gaggawa da shugabannin ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa gwamnatin ta shirya wannan taron ne a wani yunƙuri na daƙile shirin fara yajin aikin ma'aikata daga ranar 3 ga watan Oktoba, 2023.
Rahotanni sun bayyana cewa taron zai gudana idan Allah ya kaimu an jima da yammacin yau Jumu'a, 29 ga watan Satumba, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Najeriya Ta Yi Babban Rashi
An tattaro cewa taron wanda aka tsara fara wa da misalin ƙarfe 12:00 na tsakar rana, a halin yanzu gwamnati ta ɗaga shi zuwa yammaci domin bai wa ƙungiyoyin kwadago damar kiran jagororinsu da ba su a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu bayanai sun nuna cewa taron zai gudana a ɗakin taro na ofishin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila.
A cewar wasu majiyoyi, saƙon gayyata zuwa taron na gaggawa ya riski ƙungiyar NLC da takwararta TUC da safiyar nan ta Jumu'a ta hannun ma'aikatar kwadago da samar da ayyukan yi.
NLC da TUC sun cimma matsayar tafiya yajin aiki
Idan zaku iya tunawa, manyan ƙungiyoyin ma'aikatan Najeriya sun cimma matsayar tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.
A cewar shugabannin ƙungiyoyin, zasu rufe harkokin tattalin arzikin Najeriya saboda gwamnati ta gaza wajen shawo kan wahalhalun da aka shiga sakamakon cire tallafin mai.
Sun umarci rassansu na jihohi su fara shirya fita zanga-zangar lumana a faɗin ƙasar nan, kamar yadda Dailypost ta tattaro.
Kwankwaso Ya Sake Shiga Sabuwar Matsala a NNPP Bayan Taron BoT
A wani labarin kuma Kwamitin amintattu na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ya gudanar da taronsa a ranar Juma'a 29 ga watan Satumba a jihar Lagas.
NNPP ta amince tare da tabbatar da korar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, dan takararta na shugaban kasa a babban zaben 2023.
Asali: Legit.ng