"Litar Man Fetur Zata Karye Ta Dawo Naira 180 a Najeriya" Fitaccen Malami Ya Fadi Lokaci

"Litar Man Fetur Zata Karye Ta Dawo Naira 180 a Najeriya" Fitaccen Malami Ya Fadi Lokaci

  • Shahararren malamin addini mazaunin Lagas, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya ce farashin man fetur na gab da sauka a Najeriya
  • Primate Ayodele ya bayyana cewa al'ummar kasar za su fara siyan man fetur kan farashi mai rahusa sannan jin dadi zai zo masu
  • Gwamnatin tarayya ta kara farashin mai sau biyu tun bayan shigowar gwamnati mai ci a yanzu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Lagos - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya bayyana cewa farashin man fetur zai fadi warwas daga N617 kan kowace lita a yanzu zuwa N180.

Ayodele wanda ya yi hasashen a cikin wani sabon bidiyo ya bukaci yan Najeriya da su sa rai da hakan.

Primate Ayodele ya ce farashin man fetur zai koma N1809
"Litar Man Fetur Zata Karye Ta Dawo N180 a Najeriya" Fitaccen Malami Ya Fadi Lokaci Hoto: Primate Babatunde Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

"Farashin man fetur zai fadi warwas" - Primate Ayodele

A cewarsa, hasashen ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin gasar da ke tattare da daidaita farashin man fetur.

Kara karanta wannan

Masani Ya Hasko Abubuwan Da Za Su Jawo Kayan Abinci Su Yi Masifar Tsada a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A tuna cewa bayan ya hau karagar mulki, Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kara farashin man fetur daga N165 zuwa N530 zuwa sama da N600. Sakamakon haka, lamarin ya shafi harkokin tattalin arziki sosai a kasar.

Malamin addinin ya ce:

"Ina hango farashin man fetur. Yan Najeriya na bukatar kara hakuri. Farashin man fetur zai fadi warwas.
“Bari mu ce man fetur zai iya zuwa kusan 180. Amma yana iya daukar dan lokaci kadan. Amma ba mai tsayi da yawa ba. Ina tsammanin wasu watanni."

Ya kara da cewar:

"Kamfanonin da gwamnati ta ba da lasisin shigo da mai, za su karya farashin. Don haka sai mu yi kyakkyawan fata game da farashin man fetur.”

APC ta bayyana matsayar Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi watsi da iƙirarin cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sake ɓullo da tallafin man fetur ta bayan fage, inda ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta shiga tsakani ne kawai don daidaita farashinsa.

A kwanakin baya ne dai aka samu rahotannin cewa Shugaba Tinubu a watan Agusta ya amince da kashe kuɗi N169.4bn domin farashin man fetur ya tsaya a kan N620, cewar rahoton Business Day.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng