Yan Sandan Kano Sun Kwato Wayoyi 996, Kwamfuta Da Katin ATM a Hannun Barayi

Yan Sandan Kano Sun Kwato Wayoyi 996, Kwamfuta Da Katin ATM a Hannun Barayi

  • Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta kama barayin waya tare da kwato wayoyi da dama daga hannun bata gari a sassan jihar
  • Rundunar ta gano sama da wayoyin salula 996 da kwamfutoci, katinan cirar kudi daga nau'urar ATM da wasu kayayyakin daga hannun wadanda ake zargin da aikata laifuka
  • Hukumar yan sanda ta jaddada kudirinta na cigaba da tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Kano

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Rundunar yan sandan Jihar Kano ta kama wani Ibrahim Adamu da Mujittafa Sale bisa zargin satar wayoyi 996, kananan kwamfutoci, katinan cirar kudi da kuma kudi a kasuwar waya ta Farm Centre da Beirut da ke kwaryar birnin Kano.

Mai magana da ya yawun yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka ga manema labarai a Kano, da yammacin Talata.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Harbi Dalibai 3, Sun Sace Wata a Kwalejin Kimiyya a Wata Jihar Arewa

Ya ce sun karbi korafi da dama daga wanda aka balle wa shaguna aka kuma daukar mu su wayoyi na miliyoyin Naira, Daily Trust ta rahoto.

"Rundunar yan sanda ta bibiyi wani korafi da masu shagon Dansulaika GSM, da ke Farm Centre, cewa wasu da ba a san ko su waye ba sun balle shaguna 11 ta silin tare da sace wadannan abubuwa: wayoyin hannu, kwamfutar teburi da kanana da kuma kudin ciniki, katinan cirar kudi da kuma wasu abubuwan," Kiyawa.

Kiyawa ya ce wani binciken kwararru da aka gudanar ya yi silar kama wani Ibrahim Adamu dan unguwar Sallari, da ke karamar hukumar Tarauni, Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu cikin wadanda ake zargin sun amsa laifukansu

"Wanda ake zargin ya amsawa yan sanda cewa shi kadai ya aikata laifin inda aka same shi da wayoyi 106, kananan kwamfutoci 9, kudi kimanin naira 115,940, katin cirar kudi 9 da wasu kayayyakin. Za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike," in ji Kiyawa.

Kara karanta wannan

Wasu Ma Su Son Siffanta Kansu Da Karnuka Sun Yi Wata Ganawa, Sun Yi Ta Haushi Ga Junansu, Bidiyon Ya Yadu

A daya bangaren, Kiyawa ya ce

"Sun karbi wani rahoton daga kasuwar waya ta Beirut, cewa an kwashe masa wayoyi kala kala kuma yana zargin yaron shagonsa, Mujittafa Sale mai shekaru 19 dan unguwar Dukawuya.
"Bayan karbar korafin, kwamishinan yan sanda ya umarci tawaga ta musamman da ta gudanar da bincike. Yayin binciken, an kama Mujittafa Sale wanda ya amsa laifin ya kuma bayyana yadda suka hada kai da wani Ahmed Abbati, mai shekaru 23, dan unguwar Dukawuya wajen aikata laifin."

A cewarsa, an kama wanda ke taimaka masa boye wayoyin bayan an fadada bincike.

Sunayen wasu daga cikin wadanda ake zargi da satar waya a Kano

Ya bayyana sunayensu kamar haka Musa Muhammad Shafi'u, shekaru 25; Nusairu Nasiru, shekaru 22; da Usman Muhammad, dan shekara 25, dukkaninsu yan unguwar Dukawuya, Kano.

Ya kara da cewa bayan kara fadada bincike, an samu wayoyi 890 daga wajensu, kuma za a tura su kotu da zarar an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Rudani: An kwato gawar wata mata daga bakin kada, jama'a sun shiga jimami

Kiyawa ya kara da cewa yana shawartar masu shaguna da su san wanda za su bawa amanar kasuwanci yayin da yake jaddada kudirin hukumar na cigaba da tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.

Satar Waya: Fusatattun Matasa Sun Sake Kone Adaidaita Sahu Ta Barayin Waya a Kano

A wani rahoton kun ji cewa wasu fusatattun matasa sun cinnawa adaidaita sahu wuta wanda ake zargin ta masu kwacen waya ne a Kofar Kabuga a karamar hukumar Gwale da ke jihar Kano.

Abin ya faru ne a ranar Laraba 24 ga watan Mayu bayan mutanen su fahimci cewa yaran sun zo ne don kwace wayoyin mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164