Kano: Hotunan ɓarayin waya uku da aka kama bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa

Kano: Hotunan ɓarayin waya uku da aka kama bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa

  • Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 3 bisa zargin su da halaka wani Mohammed Sulaiman sannan suka tsere da wayar sa
  • Bayan sun ji lugude ne su ka bayyana cewa tabbas sun kara kai wa wani Kingsley Sunday farmaki sannan suka yi awon gaba da wayar sa
  • A ranar 20 ga watan Satumba kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana yadda lamarin ya faru a wata takarda

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wasu mutane 3 da ake zargin sun sharba wa wani Mohammed Sulaiman wuka inda hakan ya kai ga ajalin sa sannan suka gudu da wayar sa.

Kamar yadda LIB ta ruwaito, sun kara da bayyana cewa sun kai wa wani Kingsley farmaki a ranar Lahadi inda suka kwace wayar sa kuma suka tsere.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Cafke Sajan Ɗan Sanda Da Harsasai 370 a Plateau

Kano: Hotunan ɓarayin waya da aka kama a bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa
Hoton wasu barayin waya da aka kama a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa a wata takarda ta ranar Litinin, 20 ga watan Satumba ya ce sun kama wadanda ake zargin bisa laifin fashi da makami.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kano: Hotunan ɓarayin waya da aka kama a bayan sun kashe wani sun ƙwace wayansa
Bata gari da aka kama a Kano. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kamar yadda LIB ta ruwaito Kiyawa ya bayyana cewa:

“A ranar 19 ga watan Satumban 2021 da misalin karfe 11 na dare muka samu rahoton wasu batagari sun kai wa wani Mohammed Sulaiman mazaunin Sharada Quarters a Kano a daidai titin Yahaya Gusau dake Sharada inda suka datse shi da wuka kuma suka tsere da wayar sa.”
“Take a wurin aka wuce da shi asibitin kwararru na Murtala Mohammed inda aka tabbatar da rasuwar sa. Har ila yau, a ranar aka samu rahoton yadda da misalin karfe 11:20 na dare bata gari suka kara kai wa wani Kingsley Sunday mazaunin Panshekara Quarters dake Kano farmaki inda suka datse shi a kafadar sa suka tsere da wayar sa. An nufi asibitin Murtala da shi inda aka duba lafiyar sa kuma aka sallame shi.”

Kara karanta wannan

Daga bisani, NAF ta dauka alhakin yi wa farar hula ruwan wuta a Yobe

Kwamishinan bai bata lokaci ba ya tura rundunar ‘yan sanda su kama su

Bayan samun rahoton ne kwamishinan rundunar ‘yan sandar jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko ya tayar da wata runduna wacce SP Sulaiman Ibrahim ya jagoranta suka kama wadanda ake zargin.

“Cikin dabara rundunar ta kama Hussaini Malami mai shekaru 17, Harisu Manniru mai shekaru 20 da kuma Hussaini Abubakar mai shekaru 19 duk mazauna Zawaciki Quarters dake karkashin karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano. An ga wuka mai alamar jini da kuma wayoyin wadanda su ka kai wa farmakin a wurin su.
“Bayan bincike mai yawan gaske wadanda ake zargin sun bayyana cewa sun kai wa Kingsley farmaki kuma sun datse shi a kafada da goshin sa kuma suka yi awon gaba da wayar sa. Sun kuma bayar da bayanai masu amfani.”

Kwamishinan ya ce za a dauki mataki a kan su

Kwamishinan rundunar ya ce za a mayar da lamarin zuwa bangaren binciken manyan laifuka don cigaba da bincike akan su sannan kotu ta yanke mu su hukunci.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bindige soja har lahira yayin da suka sace mata da yaranta 2 a Zaria

Hotunan mutumin da aka kama ya damfari mutane 64 miliyoyin naira a Kano

A wani rahoton daban, Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani hatsabibin dan damfara bisa zargin sa da amfani da sunan babban bankin Najeriya wurin yasar dukiyar mutane 64 ta hanyar amfani da takardun bogi, LIB ta ruwaito.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a wata takarda ta ranar Laraba, 8 ga watan Satumba inda yace an kama wanda ake zargin, Buhari Hassan a Yankaba Quarters ne da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164