Mutane 6 Sun Mutu a Sabon Harin da Aka Kai Kudancin Jihar Kaduna

Mutane 6 Sun Mutu a Sabon Harin da Aka Kai Kudancin Jihar Kaduna

  • 'Yan bindiga sun yi ajalin mutane shida har da ƙananan yara a sabon harin da suka kai kudancin jihar Kaduna
  • Rahoto ya nuna maharan sun shiga kauyen Takanai, ƙaramar hukumar Zangon Kataf, inda suka buɗe wuta kan jama'a da daren Talata
  • Kakakin rundunar 'yan sanda reshen jihar Ƙaduna, Mohammed Jalige, bai ce komai ba har kawo yanzu

Jihar Kaduna - Miyagun 'yan bindiga sun halaka mutane shida da daren ranar Talata yayin da suka kai sabon harin ƙauyen Takanai, yankin Aytap da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Kaduna.

Wannan mummunan hari na zuwa ne kwanaki biyar kacal bayan wasu 'yan ta'adda sun kai farmaki garin Ƙaura, inda suka kashe wata mata kuma suka sace 'ya'yanta biyu.

Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani.
Mutane 6 Sun Mutu a Sabon Harin da Aka Kai Kudancin Jihar Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Muƙaddashin Sakataren hakimin yankin, Mista Samson Markus, ya tabbatar da sabon harin da aka kashe mutane 6 jiya da daddare ga jaridar Punch ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin Kwadago NLC da TUC Sun Ayyana Shiga Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani a Najeriya, Sun Faɗi Rana

Yadda lamarin ya faru

Ya ce 'yan bindigan sun shiga ƙauyen da misalin ƙarfe 7:00 na dare, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi, inda suka yi ajalin mutum huɗu a gida ɗaya, da ƙarin biyu a wani gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa ya ce:

"Muna cikin harkokin mu na yau da kullum kwatsam muka jiyo ƙarar harbe-harben bindiga, da farko mun yi tunanin dakarun sojoji ne daga bisani muka gane Funai ne suka shigo daga Zangon Urban."
"Kafin dakarun sojoji su ƙariso sun kashe mutane shida ciki har da ƙananan yara guda biyu. Da zuwan sojoji sai suka tsorata, nan take dukkansu suka ari na kare, suka bar ƙauyen."
“Abin takaici ne irin wannan lamari mai ban tausayi yana ci gaba da faruwa a kauyukanmu a lokacin da muke tunanin zaman lafiya ya dawo."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Gobarar Kotun Koli, Ta Bayyana Abinda Take Zargi

Mista Markus ya yi kira ga gwamnati da rundunar sojin Najeriya su kara zage dantse wajen yaƙi da waɗannan 'yan ta'adda da ke kashe mutane haka kawai.

Kakakin yan sandan Kaduna, Mohammed Jalige, bai ɗaga kiran da aka masa kan wannan sabon harin ba har kawo yanzu, jaridar Naija News ta rahoto.

Gwamna Namadi Ya Bada Hutun Kwana Daya Na Maulidi a Jihar Jigawa

A wani rahoton na daban Gwamnan Jigawa, Umar Namadi, ya ayyana ranar 12 ga watan Rabi'ul Awwal, 1445H a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jiharsa.

Ya ce gwamnatinsa ta amince da wannan hutun ne domin bada damar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad SAW.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel