Tinubu Ya Taya Al'ummar Musulmai Murnar Zagayowar Ranar Maulidi

Tinubu Ya Taya Al'ummar Musulmai Murnar Zagayowar Ranar Maulidi

  • Yayin da ake shirin bikin murnar zagayowar Maulidi a Najeriya, Tinubu ya tura sako ga Musulmai
  • A cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau, ya roki 'yan Najeriya addu'o'i ga gwamnatinsa
  • Tinubu ya kuma roki mabiya da su yi koyi da kyawawan halayen manzon Allah (SAW) na hakuri da juriya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su yi wa kasar addu'a da kuma gwamnatinsa.

Tinubu ya yi wannan rokon ne yayin taya al'ummar Musulmai murnar bikin Maulidi da za a yi gobe.yayin taya al'ummar Musulmai murnar bikin Maulidi da za a yi gobe.

Tinubu ya taya al'ummar Musulmai murnar bikin Maulidi
Sakon Tinubu Ga Al'ummar Musulmai Murnar Bikin Maulidi. Hoto: Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Meye Tinubu ya ce kan bikin Maulidi?

Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin hadiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale a yau Talata 26 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Bayyana Ranar Hutun Maulidi a Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya ce a yanzu kasar na bukatar addu'a don samun nasara wurin dakile tsaro da farfaɗo da tattalin arziki, cewar Channels TV.

Shugaban ya bukaci al'ummar Musulmai da su yi koyi da kyawawan halayen manzon tsira, Muhammad (SAW).

Ya ce:

"Mu na bukatar hadin kan 'yan Najeriya wurin kishin kasa da hakuri da kuma addu'o'i ga kasar mu.
"Mabiya ya kamata su yi koyi da koyarwar manzon Allah, Muhammad (SAW)."

Wane sako Tinubu ya tura a bikin Maulidi?

Ya ce bayan murnar ranar haihuwar ma'aiki, akwai bukatar Musulmai su dage da addu'a ga Najeriya, Premium Times ta tattaro.

Ya bukaci malaman addini da su yi addu'a ga kasar da kuma yin kira ga mabiyansu da su yi koyi da halayen manzon Allah (SAW).

Ya kara da cewa:

"Akwai babban darasi na juriya da hakuri da kan-kan da kai da kuma rashin son kai da ya kamata mu koya daga Annabi Muhammad (SAW)."

Kara karanta wannan

Zuwan Wike Abuja: Jigon APC ya fadi babban abin da Wike zai yi a matsayin minista

A karshe, shugaban ya roki mabiya da su taimaki mabukata da kuma yi wa shugabanni addu'o'i a yayin murnar bikin.

Tinubu ya ba da hutun Maulidi a Najeriya

A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya ba ayyana ranar Laraba 27 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu.

Wasu daga cikin Musulmai na bikin ranar Maulidi don murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.