An Bai Wa Hamata Iska Kan Rikicin Limancin Masallacin Juma'a A Legas

An Bai Wa Hamata Iska Kan Rikicin Limancin Masallacin Juma'a A Legas

  • Rikici ya barke tsakanin manyan limaman masallacin Juma'a a jihar Legas kan shugabanci
  • Lamarin ya faru ne a Epe da ke yankin Ita Apo a cikin jihar Legas a ranar Juma'a 22 ga watan Satumba
  • Ganin haka ne ya sa mataimakin gwamnan jihar, Obafemi Hamzat ya umarci girke jami'an tsaro a masallacin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Legas - An kai ruwa rana yayin da ake rikici kan limancin masallacin Juma'a a jihar Legas.

Wannan lamari ya faru ne a Epe da ke yankin Ita Apo a cikin jihar Legas a ranar Juma'a 22 ga watan Satumba.

Rikici ya barke kan limancin masallacin Juma'a a Legas
Rikicin Ya Barke Kan Limancin Masallacin Juma'a A Legas. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Facebook

Me ya jawo rikicin limancin masallacin a Legas?

Aminiya ta tattaro cewa wasu malamai ne guda biyu wadanda babu shiri a tsakaninsu su ke kokawar neman limancin babban masallacin Juma'an.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tashin Hankali Yayin da Wasu 'Yan Bindiga Suka Halaka Jami'an Tsaro A Kan Bakin Aiki

Rikicin ya yi kamari ne a daidai lokacin sallar Juma'a inda ko wane daga cikin limaman ke kokarin jagorantar sallar Juma'a.

Rahotanni sun tabbatar cewa jami'an tsaro sun yi cafke, Alhaji Abdullateef Oladapo, wanda shi ne limamin masallacin na ainihi.

Daga bisani ne kuma wasu malamai biyu su ke ta kokarin jan sallar Juma'an a masallacin, Daily Trust ta tattaro.

Wane mataki aka dauka kan rikicin masallacin Juma'a?

Obafemi Hamzat, mataimakin gwamnan jihar Legas, ya ba da umarnin girke jami'an tsaro domin samar da tsaro a masallacin.

Wannan na zuwa ne bayan samun rahoton rikici a masallacin kan shugabanci.

An tsige Alhaji Oladapo daga limancin masallacin ne kan zargin zafafawa da kuma fadin rai wanda tuni wanda ake zargin ya musa wannan zance.

Wani da ke zaune a yankin ya tabbatar da cewa wannan rikici ya na da tarihi tsakanin ’yan kabilar Epe-Lagos da kuma Epe-Ijebu 'yan asalin Jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Kammala Binciken Gawar Fitaccen Mawakin Nan Da Ka Tono Daga Ƙabari, Bayanai Sun Fito

An rufe masallacin Juma'a kan rikicin limanci

A wani labarin, Gwamnatin jihar Osun ta rufe wani masallacin Juma'a a Inisa da ke jihar bayan rasa rai kan shugabanci.

Gwamnatin jihar har ila yau, ta haramta yin sallar jam'i a babban masallacin Idi a cikin garin.

Wannan daukar mataki na zuwa ne bayan mutane biyu sun rasa rayukansu a yayin rikicin da ke da alaka da rikicin limanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.