Kaso 40 Zuwa 50 Na Dalibai Za Su Watsar Da Karatu Saboda Karin Kudin Makaranta, ASUU
- Yayin da gwamnati ke kara kudaden jam'o'i a Najeriya, kungiyar ASUU ta yi martani mai zafi kan haka
- Shugaban kungiyar, Farfesa Emmaneul Asodeke ya ce kaso 50 na dalibai ka iya barin karatu saboda karin
- Legit Hausa ta ji ta bakin wasu dalibai da iyaye kan lamarin da kuma kokensu a kan haka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja – Shugaban Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana cewa kaso 40 zuwa 50 za su watsar da karatu nan ba da jimawa ba.
Osodoke na magana ne kan karin kudin makarantu da Gwamnatin Tarayya ke yi a kasar inda ya ce nan da shekaru uku idan ba ta shawo kan matsalar ba, da yawa za su bar karatu.
Meye martanin ASUU kan karin kudin makaranta?
Farfesan ya yi wannan gargadi ne yayin hira da gidan talabijin na Channels a Abuja a jiya Lahadi 24 ga watan Satumba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya soki jami’o’in da karin kudade babu dalili inda ya ce ya kamata gwamnati ta samar da tsare-tsaren da za su ja hankalin dalibai ne zuwa makaranta.
Ya ce:
“Yanzu jami’o’i na kara kudaden makarantu babu dalili yayin da mafi karancin albashi bai wuce dubu 30 ba inda za ka biya haya da kuma kudin sufuri kuma ana daura hakan akan dalibai.
“Idan ba a dauki matakai ba, kaso 40 zuwa 50 na dalibai ka iya barin makaranta saboda karin kudaden.”
Osodeke ya gargadi gwamnati cewa kasar ka iya shiga halin matsala idan har matasanta ba su da ilimi kuma ba sa zuwa makaranta, Daily Trust ta tattaro.
Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a
Wane martani mutane ke yi kan karin kudin makaranta?
Legit Hausa ta ji ta bakin wasu game da kare-karen kudin makaranta da ake yi.
Mukhtari Usman dalibi a jami’ar Maiduguri ya ce gaskiya tun lokacin da ya ji wannan karin kudin hankalinsa ya tashi matuka.
Ya ce:
“Samun wannan labari ya tayar min da hankali ganin yadda mahaifina ba shi da karfin biya min, ina kira ga hukumomi su duba yiyuwar rage yawan kudaden.”
Aisha Muhammad Hussaini, daliba a Jami’ar jihar Gombe ta ce:
“Duk da dai ba a samu karin a bangare na ba amma mu na da 'yan uwa wadanda karin ya shafa kuma ba mu da halin biya musu makudan kudade haka.”
Wani daga cikin iyayen yara, Mallam Umar Abdulkadir ya ce a gaskiya gwamnati ba ta tausayin talaka, ta yaya a cikin wannan hali da ake ciki mutum zai kara kudin makaranta.
Jami’ar Legas ta rage kudin makaranta
A wani labarin, Jami’ar Legas ta rage kudin makarantar da ta kara a kwanakin baya.
Rage kudin makarantar na zuwa ne bayan dalibai sun yi zanga-zangar kin amincewa da karin.
Asali: Legit.ng