Jami'an Tsaro Sun Fatattaki Ƴan Bindigan Da Suka Yi Yunkurin Sace Mutane a Jihar Katsina
- Ƴan bindiga sun kwashi kashin su a hannu bayan sun yi yunƙurin sace mutane da dama a jihar Katsina
- Jami'an ƴan sanda, sojoji da ƴan banga ne dai suka fatattaki ƴan bindigan bayan sun kai hari a ƙaramar hukumar Malumfashi
- Jami'an tsaron sun fatattaki ƴan bindigan ne bayan sun kwashe kusan sa'a.ɗaga suna musayar wuta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kai hari a ranar Asabar da daddare a rukunin gidajen Tijjani Malumfashi, da ke cikin ƙaramar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.
Jaridar The Punch ta rahoto cewa ƴan bindigan sun yi yunƙurin yin garkuwa da mutane a yayin harin da suka kai.
Ƴan bindigan waɗanda yawansu ya kai mutum 50 sun kawo harin ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare ɗauke da manyan makamai inda suna isa suka fara harbin iska, rahoton PM News ya tabbatar.
Gwamnan Zamfara Ya Fusata Kan Satar Daliban Jami'ar Gwamnatin Tarayya, Ya Fadi Muhimmin Kokarin Da Yake Yi
Ƴan bindigan sun rarrabu inda suka riƙa bi gida-gida, suna fitar da jama’a kafin daga bisani jami’an ƴan sanda, sojoji da ƴan banga su kawo ɗauki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jami'an tsaro sun fatattaki ƴan bindigan
Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, zuwan ƴan sanda da sojoji cikin gaggawa ya ceci mutanen da aka yi yunƙurin garkuwa da su, ciki har wani alƙali (Alkali Saidu).
An tattaro cewa an fito da mutane aƙalla shida daga gidajensu, inda aka ɗaure su da rufe musu ido kafin isowar jami’an tsaro.
"DPO na ƴan sandan Malumfashi tare da tawagar ƴan sanda, sojoji da ƴan banga sun yi nasarar daƙile harin." A cewar majiyar.
"An yi musayar wuta sosai tsakanin ƴan bindigan da jami'an tsaro kusan na sa'a ɗaya kafin ƴan bindigan su ranta a na kare."
"Amma ɗaya daga cikin waɗanda harin ya ritsa da su, wani fitaccen ɗan kasuwa, Alhaji Zaharaddeen, wanda aka fi sani da Danmaliki, ƴan bindigan sun harbe shi, inda ake duba lafiyarsa a babban asibitin Kwandala da ke Malumfashi."
Yan Bindiga Sun Sace Likita a Kogi
A wani labarin kuma, ƴan bindiga waɗanda ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wani babban likita a jihar Kogi.
Ƴan bindigan sun yi awon da likitan mai suna Austin Uwumagbe, darektan asibitin Victory Hospital da ke Ogaminana, a ƙaramar hukumar Adavi ta jihar Kogi.
Asali: Legit.ng