Kamfanin Dangote Ya Samu Lambar Yabon Gwarzon Shekara, an Fadi Tasirinsa
- Kamfanin Dangote ya sake samun lambar yabon kamfanin da ya fi ko wanne samar da ayyukan yi da rike matasa a Najeriya
- An yaba da yadda kamfanin ke ba da kofofin saka hannun jari da kuma kawo hanyoyin more rayuwa ga ‘yan Najeriya da nahiyar Afrika
- Kamfanin Dangote na daga cikin kamfanonin da ke samar da kayayyakin more rayuwa, ciki har da siminti da fulawa
Jihar Legas - An ba masana’antar Dangote Industries Limited lambar yabo ta shekara domin karramawa da yaba kwazon da kamfanin ya nuna a cikin shekarar da ta gabata, Punch ta ruwaito.
A yayin bikin da aka yi a Legas, mawallafin Marketing Edge, John Ajayi ya bayyana cewa, lambar yabo da kamfanin Dangote ya samu, babbar lambar karramawa ce ta nuna ci gaba da bayar da gudunmawar da kamfanin ke yi ga ci gaban tattalin arzikin Najeriya da Afirka.
A cewar Ajayi:
"Wannan karramawa ta shafi yawancin saka hannun jari na kasuwanci da kuma sa hannun kamfanoni da kamfanin ke aiwatarwa a Afirka a matsayin nahiya."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya samarwa matasa aiki
A yayin gabatar da lambar yabon, ya danganta matsayin Dangote a matsayi na daya a tsakanin takwarorinsa a fannin samar da ayyukan yi, wanda yace ya ba matasa da dama ayyuka.
Ya kuma yabawa masana’antar Dangote bisa jajircewarsu wajen samar da muhimman ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya, National Wire ta ruwaito.
Ya ce ba da lambar yabon ya zo ne daidai bikin cika shekara 20 na Marketing Edge da kuma zagaye na 11 na lambar yabo ta Brands da Advertising Excellence Award.
An kuma ba da wasu nau'o'in iri da yawa na lambar yabo a taron ga ‘yan kasuwa da kamfanoni daban saboda rawar da suka taka a fannin kasuwanci.
Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a
An karrama Dangote a jamhuriyar Nijar
A wani labarin na daban, shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar, Mohammed Bazoum ya karrama wasu daga cikin manyan Najeriya da lambar yabo na girmamawa.
Kamar yadda Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar 3 ga watan Agusta 2022, wadanda Mohammed Bazoum ya karrama sun hada da Gwamnoni uku.
Mai girma Mohammed Bazoum ya bada lambar yabo ga Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, da Abubakar Badarun jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng