Akwai Bukatar Gyara a Najeriya, Wike Ya Zo Don Yiwa Abuja Saitin da Ya Dace, Inji Jigon APC
- Wani jigo a jam'iyyar APC, Francis Okoye ya goyi bayan aikun rusau da ma’aikatar FCTA karkashin jagorancin Nyesom Wike ta yi a Abuja
- Okoye ya ce rusau din ya yi daidai da tsarin babban birnin tarayya Abuja da yadda aka tsara birnin a takardar gwamnatin Najeriya
- A wata hira ta musamman da Legit ta yi da shi, Okoye ya ce an nada tsohon gwamnan na jihar Ribas ministan babban birnin tarayya Abuja ne domin gyara Abuja, babban birnin kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Babban jigon jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas, Francis Okoye, ya goyi bayan ministan babban birnin tarayya (FCT) Nyesom Wike kan rusa wasu haramtattun gine-gine a babban birnin kasar.
Okoye ya ce yana goyon bayan duk wani rusau da ministan babban birnin tarayya ya yi domin sun yi daidai da tsarin Abuja.
Ahaf: Tinubu ya dawo da 'yan Najeriya baya cikin bakin talauci sadda ya cire tallafin mai, malamin jami'a
Jigon na APC ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da wakilin Legit ta wayar tarho a karshen mako.
A saurarawa Wike, gyara yake, inji jigon APC
Ya shawarci mazauna garin da su rika tambayar lasisin filaye kafin su siya don gina don kasuwanci ko gida a Abuja.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Abuja tana da tsari mai girma, idan kuna son gina ko mallakar filaye, ya kamata ku bincika don sanin ko an sanya wa wurin alamar na kasuwanci ne ko kuma gini ne mai zaman kansa."
Ya kuma bayyana cewa, matukar ba a bi ka’ida ba, ministan zai ci gaba da aiki tare da rushe gine-ginen da ke kan turbayar birnin ba bisa ka’ida ba.
Wike zai gyara Abuja, inji Okoye
Okoye ya ce an nada Wike ministan babban birnin tarayya ne domin ya gyara Abuja kuma kowa ya kamata ya mara masa baya a kan hakan.
Ya kara da cewa Najeriya na bukatar gyara kuma jama’a yana da kyau su yi kokarin yin abubuwan da suka dace a koda yaushe.
A kalamansa:
“Muna bukatar gyara kasar nan kuma dole ne mu tabbatar mun yi abubuwa da suka dace domin mu gyara ta. Ba na goyon bayan mugunta ko zalunci ko a yi gini a kan kasar da bata dace a gina ba. Wike ya zo gyara Abuja ne, dole mu ba shi wannan goon baya.”
Wike ya kwace filayen su Peter Obi a Abuja
A wani labarin, ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya soke takardun wasu filaye 165 a Abuja saboda rashin bunkasa su.
Sakataren dindin na birnin tarayya, Olusade Adesola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 21 ga watan Satumba, jaridar Premium Times ta rahoto.
Filayen da abun ya shafa suna a yankunan Maitama, Gudu, Wuye, Katampe Extension, Wuse 2, Jabi, Utako, Idu Industrial Zone, da Asokoro.
Asali: Legit.ng