'Yan Najeriya Sun Kara Gigicewa Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Malamin Jami’a Ya Ba da Shawari

'Yan Najeriya Sun Kara Gigicewa Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Malamin Jami’a Ya Ba da Shawari

  • Malami daga jami’ar Kaduna ya bayyana kadan daga abin da ya hango bayan da gwamnatin Najeriya ta janye tallafin mai
  • A cewarsa, hakan ya jefa ‘yan kasar cikin tashin hankali da karuwar talauci, lamarin da ke kara jefa al’umma a cikin wahala
  • Ya zuwa yanzu, ana siyar da man fetur sama da N620 a Najeriya, kayayyaki sun kara farashin da kowa ke ci gaba da kokawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Godwin Kwalbe, wani mlamin jami'a ya shawarci gwamnati a dukkan matakai kan yadda za a yi a magance matsalar talauci da ke addabar dimbin al’ummar kasar nan.

Mista Kwalbe, malami a sashin tarihi na Jami’ar Jihar Kaduna, ya ba da wannan shawarar ne a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Abuja ranar Lahadi.

Ya ce hanyar magance matsalar bakin talauci ta ba da tallafin wucin gadi ba shi ne mafita ba, domin hakan ya nuna kamar ana yiwa talaucin kallon na lokaci zuwa lokaci ne, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Rudani: An kwato gawar wata mata daga bakin kada, jama'a sun shiga jimami

Talaucin da 'yan Najeriya suka shiga sakamakon cire tallafin man fetur
Yadda ake talauci a Najeriya | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Cire tallafn mai ya jefa 'yan kasa a bakin talauci

Ya ce cire tallafin man fetur bai haifar da kunci ko fatara kadai ba, ya kai ga kara jefa ‘yan kasa cikin kangin talauci mara dadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malamin ya yi nuni da cewa, fiye da rabin al'ummar kasar na fama da bakin talauci, inda yace wasu da aka haifa a cikin talauci akwai yiwuwar su ci gaba da rayuwar wahala har karshen rayuwarsa.

Ya yi nuni da cewa, Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da shirye-shirye da dama na rage radadin talauci a kokarinta na magance talauci.

Ina mafita ga matsalolin talauci?

Ya ambaci yadda gwamnatin Najeriya ta yi ta ba da tallafi irin na Korona da sauransu, amma duk da haka talauci bai kau ba.

A cewarsa, dukkan wadannan shirye-shiryen tallafi na gwamnati ba a tsara su ta yadda za su kawo karshen talauci ba, sai dai su rage na dan lokaci.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Malaman jami'a sun ci taliyar karshe saboda aikata badala da rashawa

Ya shawarci gwamnatin tarayya da jihohi da kananan hukumomi da su koma su natsu su fito da tsare-tsare masu kyau na fitar da jama’a daga kangin wahala.

Illar talauci ga mutanen kasa

A wani labarin, kunci cewa, talauci da rashin aikin yi ga matasa sune manyan dalilan da suke kawo shan miyagun kwayoyi da kayan maye a kasar nan, kamar yanda hukumar lafiya ta yankin Afrika ta yamma ta bayyana.

Tayi kira da a dauki matakin gaggawa gurin samar da daidaitaccen yanayin samar da kwayoyin da zasu amfani lafiya, tsaro da kuma zaman lafiyar yan Najeriya.

Hukumar ta jinjiinawa kokarin da gwamnatin tarayya, ma'aikatar lafiy , hukumar NAFDAC da kuma NDLEA suke gurin yaki da kalubalen da ake fuskanta na shan miyagun kwayoyi da kuma safarar su a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.