Talauci: Najeriya ta doke kasar Indiya, ta zama zakara a Duniya – Rahoto na musamman

Talauci: Najeriya ta doke kasar Indiya, ta zama zakara a Duniya – Rahoto na musamman

- Najeriya ta doke kasar Indiya a matsayin kasar da ta fi yawan talakawa a Duniya

- A wani rahoto na musamman da cibiyar Brookings Institution ta fitar a karshen watan Mayu, Najeriya na da yawan tyalakawa miliyan 87 yayin da Indiya ked a mutum miliyan 73

- Rahoton ya bayyana cewar jamhuriyar dimokradiyar Kongo zata hau mataki na 2 nan bada dadewa ba

A wani rahoto na musamman da cibiyar Brookings Institution ta fitar a karshen watan Mayu na shekarar nan ya bayyana Najeriya a matsayin kasa ta daya a duniya a yawan mutanen dake zaune cikin tsananin talauci.

Talauci: Najeriya ta doke kasar Indiya, ta zama zakara a Duniya – Rahoto na musamman

Talauci: Najeriya ta doke kasar Indiya, ta zama zakara a Duniya – Rahoto na musamman

Najeriya ta doke kasar Indiya a mataki na daya da yawan mutane dake zaune cikin kangin talauci da adadin mutane miliyan 14. Yanzu Najeriya ce a gaba da adadin talakawa miliyan 87 yayin d Indiya keda mutane miliyan 73.

DUBA WANNAN: ‘Gyauron ‘yan PDP ke bata mana akidar jam’iyyar APC’ – Tinubu

Jaridar The Cable ta rawito cewar kasar Indiya ta dade a mataki na daya da adadin talakawa biliyan 1.324 a lokacin da Najeriya keda mutane miliyan 200.

A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, shugaba Buhari ya bayyana cewar babu wanda zai iya daure shi bayan ya kamala wa’adin mulkin sa saboda ya tsare mutunci da kimar sa.

Buhari ya bayyana cewar da bai kiyaye mutuncin sa ba a mukaman day a rike a baya, da tuni ya dade a garkame a gidan yari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel