Gwamnan Jihar Zamfara Ya Yi Allah Wadai Da Sace Daliban Da Yan Bindiga Suka Yi a Jihar
- Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya nuna takaicinsa da baƙin cikinsa kan satar ɗalibai mata na jami'ar gwamnatin tarayya da ƴan bindiga suka yi
- Gwamnan ya yi Allah wadai da harin na ƴan bindiga inda ya bayyana shi a matsayin aikin matsorata
- Dauda ya bayyana cewa jami'an tsaro na cigaba da aiki tuƙuru ta sama da ta ƙasa domin ganin sun ceto ɗaliban da ke hannun ƴan bindigan cikin ƙoshin lafiya
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi Allah wadai da sace daliban jami'ar gwamnatin tarayya ta Gusau da aka yi a a cikin ƴan kwanakin nan.
A daren ranar Juma'a, 22 ga watan Satumba ne dai wasu ƴan bindiga suka kai hari a Sabon-Gida cikin ƙaramar hukumar Bungudu, inda suka yi garkuwa da dalibai mata sama da mutum 24 na jami’ar.
Da yake nuna takaicinsa kan lamarin, gwamnan ya bayyana harin a matsayin aikin 'matsorata.'
Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da su kuɓutar da daliban da ke riƙe a hannun ƴan bindigan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Gwamna Dauda ya yi Allah wadai da harin
Gwamna Dauda ya bayyana hakan ne a wani rubuta da ya yi a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).
“Na yi matukar baƙin ciki da harin da matsoratan ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Sabon Gida inda suka yi garkuwa da wasu mazauna garin da wasu ɗalibai mata."
"Nan take muka tura jami’an tsaro waɗanda suka yi nasarar ceto wasu daga cikin waɗanda harin ya ritsa da su, kuma har yanzu suna cigaba da bin miyagun ta ƙasa da sama."
"Na kasance cikin tuntuɓar shuwagabannin tsaro na jihar da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawowar duk sauran wadanda abin ya shafa cikin ƙoshin lafiya da kawar da lamarin cikin gaggawa Insha Allah."
Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023
Matsalar tsaro sai dai addu'a
Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gusau, mai suna Jamilu Abdullahi, wanda ya bayyana cewa matsalar tsaro ta kai inda ta kai, sai dai a bi da addua kawai.
Jamilu ya yaba da irin ƙoƙarin da gwamnan jihar da jami'an tsaro suke yi domin ganin sauran ɗaliban da ke a hannun ƴan bindigan sun kuɓuta.
Yan Bindiga Sun Sace Ma'aikata a Jami'ar Gwamnatin Tarayya
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun sake dira a jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, inda suka yi awon gaba da wasu ma'aikatan gini.
Ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutum tara masu yin aikin gini a jami'ar bayan sun sace wasu ɗalibai mata.
Asali: Legit.ng