Gwamna Yahaya Bello Ya Bayyana Burinsa Bayan Kammala Mulkin Jihar Kogi
- Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya ce ba shi da wani buri na siyasa bayan ya bar muƙamin gwamna
- Gwamna Bello ya bayyana cewa burinsa a yanzu shine ya taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu nasara
- Ya bayyana cewa idan har shugaba Tinubu ya samu nasara a matsayinsa na shugaban ƙasa to duk ƴan Najeriya sun yi nasara
FCT, Abuja - Gwamna Yahaya Bello ya bayyana burinsa bayan ya bar kujerar gwamnan jihar Kogi.
Gwamnan ya bayyana cewa ba shi da wani buri na siyasa a yanzu.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana a wajen wani taron shekara-shekara karo na uku na 'GYB for Nigeria’s Political & Crime Correspondents/Editors' a birnin tarayya Abuja, a ranar Asabar, 23 ga Satumba, cewar rahoton Vanguard.
Burina shine in goyi bayan Shugaba Tinubu, Yahaya Bello
Gwamna Bello ya ce ba shi da wani buri na siyasa a yanzu wanda ya wuce ya taimaka wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samun nasara a mulkinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce yana shirin taimakawa Shugaba Tinubu ne domin nasararsa, nasara ce ta dukkanin ƴan Najeriya.
APC ce za ta lashe zaben gwamnan Kogi
A cewar rahoton Premium Times, gwamna Bello ya bayyana ƙwarin gwiwarsa kan cewa jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kogi, ita ce za ta lashe zaɓen gwamnan da za a yi a watan Nuwamba.
Gwamnan ya ce ɗan takarar jam’iyyar APC, Usman Ododo, zai yi nasara ne saboda haɗin kan da jam’iyyar take da shi.
"Na gode wa Allah bisa nasarorin da na samu a matsayina na gwamnan Kogi. Na san inda na tarar da jihar kuma ina farin ciki da inda na kai jihar."
Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023
"Na yi amanna cewa ɗan takarar jam'iyyar APC, Usman Ododo, zai ɗora daga kan ingantaccen ginin da muka fara a jihar Kogi."
Yan Majalisa Sun Musanta Batun Tsige Mataimakin Gwamna
A wani labarin na daban kuma, ƴan majalisar dokokin jihar Ondo, sun musanta batun karɓar cin hanci domin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.
Shugaban masu rinjaye na majalisar shi ne musanta zargin da aka yi na cewa an ba kowanensu N5m domin su tsige mataimakin gwamnan.
Asali: Legit.ng