Yan Majalisar Dokokin Jihar Ondo Sun Karbi Cin Hanci Domin Tsige Mataimakin Gwamna? Gaskiya Ta Fito

Yan Majalisar Dokokin Jihar Ondo Sun Karbi Cin Hanci Domin Tsige Mataimakin Gwamna? Gaskiya Ta Fito

  • Ƴan majalusar dokokin jihar Ondo sun musanta batun cewa an cika musu aljihunansu da kuɗaɗe domin tsige mataimakin gwamnan jihar
  • Wata ƙungiya ce dai ta yi zargin cewa an ba ƴan majalisun N5m kowanensu domin tsige mataimakin gwamnan
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar ya bayyana zargin a matsayin wani yunƙuri na ɓata sunan majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ondo - Wata ƙungiya mai suna Ondo for Better Life, a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba, ta zargi ƴan majalisar dokokin jihar Ondo da karɓar N5m domin tsige mataimakin gwamnan jihar, Lucky Aiyedatiwa.

Sai dai majalisar ta yi watsi da wannan ikirarin, tana mai cewa wani yunkuri ne na ɓata mata suna.

Yan majalisa na shirin tsige Aiyedatiwa
Yan majalisar dokokin jihar Ondo sun musanta karbar cin hanci domin tsige Aiyedatiwa Hoto: Lucky Aiyedatiwa
Asali: Twitter

A ranar Laraba ne majalisar ta fara yunƙurin tsige mataimakin gwamnan bisa zarginsa da tafka magudi a lokacin da ya riƙe muƙamin gwamna Oluwarotimi Akeredolu.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Wani Babban Likita Da Ake Ji Da Shi a Jihar Arewa

Jaridar The Punch ta ce kodinetan ƙungiyar, Mista Felix Lewis, wanda ya yi magana a Akure, babban birnin jihar a ranar Asabar, ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna da kyawawan bayanai da ke nuna cewa sun ba duk ƴan majalisar da ke goyon bayan tsigewar N5m don gudanar da aikin. Shugabannin majalisar da wasu daga cikin mambobin majalisar zartaswa na jihar ne ke gudanar da aikin."
"Mun san suna iya musanta hakan amma hakan shi ne gaskiya. Su fito su rantse idan wannan ba gaskiya ba ne."

Shin da gaske majalisar ta karɓi cin hancin N5m?

A halin da ake ciki, shugaban masu rinjaye na majalisar, Mista Oluwole Ogunmolasuyi, ya musanta wannan zargi, yana mai cewa ba zai yiwu a yi wa majalisar ƙage ba.

"Ta yaya hakan (cin hanci) zai yiwu? Mu daina magana game da wannan. Wannan ƙage ne kawai. Matsalar nan ita ce mun ƙalubalance shi (mataimakin gwamna). Akwai zargin da ake masa, sannan da zarar an tunkare ka da wani zargi, ka fito da gaskiyarka ka kare kanka."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Maida Martani Bayan Kotun Zabe Ta Yanke Hukunci Kan Nasarar Da Ya Samu a 2023

"Bugu da ƙari, maigirma gwamna ba ya da hannu a cikin wannan. Har yanzu abin da muke yi yana a ƙarƙashin ofishinmu ne."
"Ni a wajena, akwai zargi a gabanmu, yana ɗauke da sunan wani, mutumin da ya riƙe da muƙamin mataimakin gwamna, don haka ba za mu iya kawar da kai ba."
"A ce an ba mu cin hancin N5m ɓata suna ne kuma ba za mu bari a ɓata mana suna ba saboda muna yin aikinmu."

Jigon APC Ya Bayyana Dalilin Dukan Ƙwamishina

A wani labarin kuma, jigon jam'iyyar APC a jihar Ondo, Olumide Awolumate, ya bayyana dalilin da ya sanya ya lakaɗawa kwamishiniyar mata, Misis Julian Osadahun dukan tsiya.

Olumide ya yi bayanin cewa kwamishiniyar da ɗanta ne suka iske shi har gida suka fara dukansa bayan sun samu saɓani kan rabon kayan tallafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng