Gobara Ta Kone Mutum 35 a Wata Ma'ajiyar Man Fetur a Jamhuriyar Benin

Gobara Ta Kone Mutum 35 a Wata Ma'ajiyar Man Fetur a Jamhuriyar Benin

  • An samu tashin wata mummunar gobara a wata ma'ajiyar adana man fetur da aka yi fasawaurinsa daga Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
  • Gobarar ta tashi ne a ma'ajiyar da ke a garin Seme-Krake wanda ke bakin iyaka tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin
  • Mutum 35 ne dai suka ƙone ƙurmus a dalilin gobarar yayin da wasu mutane masu yawa suka samu munanan raunika

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jamhuriyar Benin - Aƙalla mutum 35 ne suka ƙone ƙurmus a Seme-Krake da ke jamhuriyar Benin bayan gobara ta tashi wata ma'ajiyar adana man fetur da aka yi fasaƙwaurinsa daga Najeriya.

Lamarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 9.30 na safiyar ranar Asabar, shi ne gobara mafi muni da ta ɓarke a ƙasar a bana.

Gobara ta tashi a Jamhuriyar Benin
Mutum 35 suka kone kurmus a gobarar Hoto: PMnews.com
Asali: UGC

Kimanin wasu mutum 40 da suka jikkata sakamakon gobarar, an kwashe su daga wurin zuwa cibiyar Asibitin Queme, a cewar rahoton Aljazeera.

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da gobara ta lamushe fitaccen kamfanin robobi a jihar kasuwanci

Da farko dai gidan rediyon Bip ya bayar da rahoton mutuwar mutum 34, inda ya ce an samu hasarar rayuka da dama duk da cewa jami’an kashe gobara sun shiga tsakani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Ministan harkokin cikin gida Alassane Seidou ya shaidawa manema labarai cewa:

"An samu mummunar gobara a garin Seme Podji. Abin takaici mun samu mutuwar mutane 34 ciki har da jarirai biyu. Gawarwakinsu sun ƙone saboda musabbabin tashin gobarar man fetur ne."

A wani ƙarin bayani, mai shigar da ƙara Abdoubaki Adam-Bongle na ma’aikatar shari’a ya ce aƙalla mutum 35 ne suka mutu a gobarar, yayin da ake sauke man fetur a cikin ma’ajiyar.

Adam-Bongle a cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ya bayyana cewa:

"Gobarar ta ƙone ma'ajiyar kuma a bisa binciken farko ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 35 ciki har da yaro ɗaya."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mummunar Gobara Ta Tashi a Wata Babbar Masana'anta Da Ake Ji Da Ita a Najeriya

Ya ce an fara gudanar da bincike domin gano musabbabin tashin gobarar.

Gobara Ta Tashi a Wata Masana'anta

A wani labarin kuma, wata mummunar gobara ta tashi a masana'antar sarrafa robobi ta Mega Plastics da ke a jihar Legas.

Gobarar ta tashi ne a ɓangaren ma'ajiyar masana'antar wacce ke a kusa kwanar titin Ilupeju a yankin Mushin na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng