Kotun Zabe Za Ta Yanke Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Legas a Ranar Litinin
- Kotum da ke sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas ta sanar da ranar yanke hukuncinta
- Kotun ta bayyana ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncinta kan ƙararrakin da ke gabanta
- Ƴan takarar jam'iyyun Labour Party da PDP ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun suna ƙalubalantar nasarar da gwamna Sanwo-Olu na APC ya samu
Jihar Legas - Kotun sauraren ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Legas na shirin yanke hukunci kan ƙararrakin da ke ƙalubalantar nasarar gwamna Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC a zaɓen ranar 18 ga watan Maris, cewar rahoton PM News.
Ƴan takarar gwamna na jam'iyyar Labour Party (LP), Gbadebo Rhodes-Vivour, da takwaransa na jam'iyyar PDP, Olajide Adediran, wanda aka fi sani da Jandor sune suka shigar ƙararrakin.
Kotun ta bayyana cewa za ta yanke hukuncin na ta ne a ranar Litinin, 25 ga watan Satumban 2023, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Shugaban kotun mai shari'a Arum Ashom, shi ne ya sanar da hakan ga dukkanin ɓangarorin a ranar Asabar, 23 ga watan Satumba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Menene dalilin shigar da ƙarar?
Rhodes-Vivour da Jandor suna ƙalubalantar ayyana gwamna Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa Obafemi Hamzat na Jam’iyyar APC a matsayin waɗanda suka lashe zaben gwamnan Jihar Legas da hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi.
Idan ba a manta ba dai a ranar 12 ga watan Agusta, lauyoyin ɓangarorin suka kammala gabatar da bayanansu a gaban kotun.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Sanwo-Olu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Gwamna Sanwo-Olu dai ya lashe zaɓen da gagarumin rinjaye, inda ya doke Rhodes-Vivour na jam'iyyar Labour Party wanda ya zo na biyu.
Gwamnan ya samu ƙuri’u 762,134 inda ya doke Rhodes-Vivour wanda ya samu ƙuri’u 312,329. Jide Adediran (Jandor) na PDP ya zo na uku inda ya samu ƙuri’u 62,449.
Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamnan APC
A wani labarin kuma, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Benue, ta tabbatar da nasarar da gwamna Hyacinth Alia na jam'iyyar APC ya samu a zaɓen gwamnan jihar.
Kotun zaɓen ta yi fatali da ƙarar da jam'iyyar PDP da ɗan takararta Titus Uba suka shigar suna ƙalubalantar nasarar gwamnan.
Asali: Legit.ng