Matashiya Ta Girka Abinci Iri-Iri, Ta Ce Kudinsu Miliyan 3.2
- Wata shahararriyar mai girka abinci yar Najeriya ta baje kolin abinci iri-iri a gidan abincinta sannan ta bayyana cewa farashinsu gaba daya miliyan 3.2 ne
- Matashiyar ta fada ma mutane cewa daga cikin abubuwan da ta girka akwai shinkafa dafa duka da miyan agushi da namomi iri-iri
- Yan Najeriya sun gaza yarda cewa za a iya kashe miliyan 3.2 a kan abinci kawai, yayin da suka fafata da ita sashin kwamet
Wata yar Najeriya mai girke-girke ta haddasa cece-kuce a tsakanin mutane bayan ta wallafa bidiyon abinciki da ya kai sama da naira miliyan 3.
Mai girkin (@hotmbycheft) ta sanar da cewar ranar zagayowar haihuwarta ne yayin da ta jefa abinciki a kan teburinta da taimakon hadimanta.
An baje kolin shinkafa dafa duka da soyayyiyar shinkafa
Daga cikin abincin da aka jera akwai robar soyayyiyar shinkafa wato 'fried rice', dafa-dukan shinkafa, miyan kaza da miyan agushi da dai sauransu a kan tebur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan Najeriya da dama sun cike da mamakin cewa wannan abincin zai iya kaiwa miliyoyin nairori. Wasu kuma sun ce farashin ya yi kadan.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
Olatunsam ta ce:
"Akalla dai wannan ya fi siyan kifi daya a kan naira miliyan 6.8. Ya kamata Ola na Lagos ya ga wannan."
iyiolakolawolebob ya tambaya:
"Yaushe kika zama Ola na Lagos."
Chiamaka ta ce:
"Na san abinci yana da tsada amma wannan farashin ya wuce gona da iri."
Gentuuu ta ce:
"Wannan abun gaba daya 500k."
Kim namjoon ta ce:
"Bikina ya tara baki fiye da 700, Miliyan 2 da doriya aka kashe dai. Lallai da alama abokan kasuwancinki masu kudi ne."
Jane windy ta ce:
"Miliyan 3.2 nawa ake bayar da hayar kauyena gaba daya Allah ya ba da sa'a."
Budurwa ta baje kolin katafaren gidan da za a siyar miliyan 1.5
A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa hotunan wani katafaren gida a Twitter sannan ta ce kudin da za a siyar da shi naira miliyan 1.5.
Matashiyar, @shalomdfirst, ta haddasa cece-kuce da wannan ikirari nata, yayin da mutane da dama suka ki yarda da maganarta.
Asali: Legit.ng