“Ba Mu Kama Alkalin Kotun Zaben Gwamnan Kano Ba”, DSS Ta Magantu

“Ba Mu Kama Alkalin Kotun Zaben Gwamnan Kano Ba”, DSS Ta Magantu

  • Hukumar DSS ta magantu kan zargin kama daya daga cikin alkalan kotun zaben gwamnan jihar Kano
  • Hukumar tsaron farin kaya ta bayyana ikirarin cewa jami'anta sun kama alkalin kotun zaben a matsayin abun dariya
  • Kakakin gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature ya zargi rundunar tsaron da razana alkalan kotun zaben don su tsige Abba Kabir Yusuf

Hukumar tsaron farin kaya wato DSS, ta karyata wani rahoto da ke cewa jami’anta sun kama daya daga cikin alkalan kotun zabe da suka yanke hukunci kan zaben gwamnan jihar Kano.

DSS ta yi watsi da rahoton ne yayin da take karyata ikirarin da gwamnatin jihar Kano ta yi cewa an kama daya daga cikin alkalan da suka soke nasarar zaben Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaben ranar 18 ga watan Maris.

Hukumar DSS ta karyata kama alkalin kotun zabe
“Ba Mu Kama Alkalin Kotun Zaben Gwamnan Kano Ba”, DSS Ta Magantu Hoto: @deji_lambo
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar PM News ta rahoto, babban sakataren gwamnan Kano da aka tsige, Sanusi Bature ne yay i zargin bayan tsige Abba Gida Gida.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: NNPP Ta Yi Martani Ga Hukuncin Tsige Abba Gida Gida, Ta Bayyana Yadda Kotun Zabe Ta Yi Wa APC Aiki

Bature ya yi ikirarin cewa hukumomin tsaro sun razana mambobin kotun zaben gwamnan jihar Kano don su yanke hukuncin da ba zai kai nasara bangaren ubangidansa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

DSS ta ce bata kama alkalin kotun zaben gwamnan Kano ba

Kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya karyata ikirarin kakakin gwamnan na jihar Kano, rahoton PRNigeria.

Afunanya ya ce:

“Wannan magana ce mai ban dariya. Kame alkalai akan wane dalili? Ba gaskiya bane, don Allah.”

Ba mu san daga ina aka yanke hukuncin zaben gwamnan Kano ba, Kakakin Abba gida gida

Da yake zantawa da Channels TV, Sanusi Bature ya ce:

“Hukumar DSS ta kama daya daga cikin alkalan da suka yanke hukunci a Kano kuma ina ganin cewa hakan tsoratarwa ce.
“Hatta ga wannan hukuncin yanar gizon da suka yanke, ba mu san daga ina suka yanke shi ba. Watakila, sun yanke hukuncin bisa tilas ko wani abu, ban tabbatar ba. Ba mu san daga wurin da suka yanke hukuncin ba kuma bamu san yanayinsu ba saboda ganinsu kawai muka yi a talbijin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Saka Dokar Kulle Na Awanni 24 a Jihar Kano

“Abubuwa da dama sun faru a bayan fage kuma ga mamakinmu, wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben baya ma cikin shari’ar. Gawuna ya yi takara a zaben, ya amshi shank aye, sannan ya taya Abba Kabir murna kuma cewa ba zai je kotu ba.”

Gwamna Abba kabir ya sha slwashin dawo da nasararsa da kotu ta kwace

A wani labarin, mun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu sannan ya sha alwashin bin hanyar da doka ta tanada wajen dawo da nasararsa da aka ƙwace.

A ranar Laraba, 20 ga watan Satumba ne dai kotun sauraron ƙarrakin zaɓen gwamnan jihar ta tsige gwamna Yusuf, tare da ba da umarnin a ba wa Nasir Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC takardar shaidar cin zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng