Rundunar 'Yan Sanda A Kano Ta Janye Dokar Hana Fitar Da Ta Kafa
- Jami'an 'yan sanda a jihar Kano sun sanar da dage dokar hana fita a birnin da aka sanya jiya Laraba a jihar bayan yanke hukunci
- Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa shi ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a yau Alhamis 21 ga watan Satumba
- Wannan na zuwa ne bayan sanya dokar hana fita a jiya Laraba 20 ga watan Satumba bayan hukuncin kotun da ta tsige Abba Kabir
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta sanar da janye dokar hana fita ta tsawon sa'o'i 24 da aka sanya jiya Laraba 20 ga watan Satumba a jihar.
Kakakin rundunar a jihar, SP Abdulahi Haruna Kiyawa shi ya sanar da haka a shafinsa na Facebook a yammacin yau Alhamis 21 ga watan Satumba.
A yaushe aka sanya dokar a Kano?
A jiya Laraba 20 ga watan Satumba ne dai rundunar ta sanya dokar bayan yanke hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben gwamna.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An sanya wannan dokar ce bayan yanke hukuncin kotu a jihar saboda gudun kada rikici ya tashi sakamakon hukuncin kotun a jiya.
Kotun a jiya ta tsige Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP tare da tabbatar da Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zabe, Daily Post ta tattaro.
Meye dalilin sanya dokar a Kano?
Rundunar 'yan sanda ta ce ta saka dokar ce don hana zirga-zirga wanda ka iya jawo rikici a jihar ganin yadda mutane su ka harzuka da shari'ar.
Tun bayan sanar da hukuncin kotun, ake zaman dar-dar musamman tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da NNPP a jihar.
Abin mamaki mutane sun yi biyayya ga dokar dai-dai gwargwado har zuwa lokacin da aka janye dokar.
An kafa dokar hana fita a jihar Kano
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta kafa dokar hana fita a jihar tun bayan yanke hukunci a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan an tsige Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP daga mukaminsa na gwamna a jihar.
Yayin hukuncin har ila yau, kotu ta tabbatar da Nasiru Gawuna na APC a matsayin wanda ya lashe zabe.
Asali: Legit.ng