Gawuna Ya Yi Rawa Bayan Nasara a Kotun Zabe? Gaskiya Ta Bayyana

Gawuna Ya Yi Rawa Bayan Nasara a Kotun Zabe? Gaskiya Ta Bayyana

  • An yi ta yaɗa wani bidiyo a shafukan sada zumunta na wani mutum yana tiƙar rawa wanda aka ce Nasiru Yusuf Gawuna ne
  • An bayyana cewa Gawuna ya tiƙi rawar ne a cikin bidiyon saboda murnar nasarar da ya samu a kotun zaɓe kan gwamna Abba Kabir
  • Sai dai, binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba Gawuna ba ne a cikin bidiyon, kuma an yaɗa bidiyon ne domin kawo ruɗani

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wani faifan bidiyo na wani mutum mai gemu yana tiƙar rawa da ake zargin ɗan takarar jam'iyyar APC a zaben watan Maris, Nasiru Yusuf Gawuna, ne ya yaɗu a shafukan sada zumunta.

A cikin bidiyon mai tsawon minti daya da daƙiƙa huɗu, an nuna mutumin mai gemu launin toka mai kama da na ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar APC, cikin murna yana tiƙar rawa.

Kara karanta wannan

Bayan Abba Gida-Gida, Kotun Zabe Ta Ƙara Yanke Hukunci Kan Nasarar Gwamnan PDP

Gawuna bai yi rawa ba bayan nasara a kotu
Bidiyon da ake cewa Gawuna ya yi rawa na karya ne Hoto: Nasiru Yusuf Gawuna
Asali: Facebook

Bidiyon da aka riƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta musamman Facebook da Twitter yana dauke da taken:

"Haɗu da Nasiru Gawuna na APC wanda ya kayar da Abba Kabiru Yusuf a kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano. Gwamna Adeleke ya samu daidai da shi a APC."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar mutanen da suka yada faifan bidiyon, Gawuna na murnar sakamakon kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna ne wacce ta kori babban abokin hamayyarsa a zaben.

Ba Gawuna ba ne a cikin bidiyon

Bidiyon da ake yaɗawan a kafafen sada zumunta an ce martani ne kan hukuncin kotun, amma binciken da Daily Trust ta yi ya nuna cewa faifan bidiyon ya riƙa yawo tun kafin hukuncin kotun.

Hakazalika, binciken da aka yi ya nuna cewa mutumin da ke cikin bidiyon zai iya yin kamanceceniya da Gawuna, amma ba shi ɗan takarar gwamnan ba ne.

Kara karanta wannan

Mai Shari'a Tsammani Ya Nemi Yan Najeriya Su Yafe Wa Tinubu Kan Laifin Safarar Kwayoyi? Gaskiya Ta Bayyana

Jaridar ta tabbatar da cewa mutumin da yake rawa a faifan bidiyon da ake yadawa ba Nasiru Yusuf Gawuna ba ne, don haka zancen karya ne kuma an raba shi ne domin a kawo ruɗani.

Gawuna Ya Magantu Kan Daukaka Karar Abba

A wani labarin kuma, Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC wanda kotu ta ayyana a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan Kano, ya yi magana kan ɗaukaka ƙarar da gwamna Abba Kabir ya ce zai yi.

Gawuna ya bayyana cewa ko kaɗan ba ya tsoron ɗaukaka ƙarar da gwamnan ya ce zai yi domin duk abin da zai faru dama can haka Allah ya tsara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng