An Tsinci Gawar Fitaccen Dan Jaridan Da Ya Bace a Zamfara

An Tsinci Gawar Fitaccen Dan Jaridan Da Ya Bace a Zamfara

  • Bayan kwana uku ana neman ɗan jarida mai aiki da jaridar Muryar Najeriya (VON), an ci karo da gawarsa
  • An gano gawar Alhaji Hamisu Danjibga a cikin wani rami da ke bayan gidansa bayan miyagu sun halaka shi
  • Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen jihar Zamfara ta tabbatar da kisan na sa inda ta buƙaci jami'an tsaro da su gudanar da bincike domin zaƙulo makasansa

Jihar Zamfara - Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen jihar Zamfara ta tabbatar a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, da kashe Alhaji Hamisu Danjibga, wakilin muryar Najeriya VON a jihar.

Jaridar Tribune ta rahoto cewa a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jihar, Ibrahim Ahmad ya fitar a Gusau, ya ce an tsinci gawar marigayin ne a wani rami da waɗanda suka kashe shi suka jefa shi a ciki.

Kara karanta wannan

"Akwai Kura-Kurai": Gwamna Abba Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu, Ya Bayyana Mataki Na Gaba Da Zai Dauka

An tsinci gawar dan jaridan da ya bace a Zamfara
Dan jaridan ya yi kwana uku ba a san inda yake ba Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

“An gano gawar tasa ne sakamakon wani wari mara daɗi da yaran makarantar Islamiyya suka ji a bayan gidansa da yammacin ranar Laraba, 20 ga Satumba, 2023."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan an buɗe ramin, iyalansa da maƙwabta sun tabbatar da cewa gawar ta Danjibga ce."

An dade ana nemansa

Jaridar Channels tv ta ce Danjibga ya shafe kwanaki uku ba a san inda yake ba kafin a gano gawarsa.

Majiyoyi sun ce da farko an tuntubi iyalansa su biya naira miliyan ɗaya domin a sake shi, amma waɗanda ba a san ko su wanene ba da suka halaka shi sai suka ƙara yawan kuɗin.

Rundunar ƴan sandan jihar ta cafke mutum ɗaya da ake zargi yana da hannu wajen kashe ɗan jaridan.

NUJ ta aike da saƙon ta'aziyya

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Jihar Arewa, Sun Sace Mahaifi Tare Da Diyarsa

Ƙungiyar ta NUJ ta mika ta'aziyyarta ga iyalan mamacin, VON, da daukacin al'ummar Zamfara.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci jami'an tsaro da su gudanar da bincike domin zaƙulo waɗanda ke da hannu wajen aikata wannan ɗanyen aikin.

Tuni dai aka yi wa marigayin jana'iza kamar yadda shari'ar addinin musulunci ta tanada.

Gwamna Dauda Zai Dauki Yan Sakai a Zamfara

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa zai ɗauki ƴan sakai a jihar domin murƙushe ƴan ta'adda.

Ya ce wannan wani ƙuduri ne da gwamnatinsa ke da shi na ganin ta kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta ƙo ci ta ƙi cinyewa a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng