Bidiyon Yadda Ganduje Da Gawuna Suka Yi Murnar Nasara a Kotu Ya Bayyana
- Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta soke nasarar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu a zaɓen gwamna na ranar Asabar, 18 ga watan Maris
- A wani sabon hukunci da kotun ta yanke, ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan a jihar
- Kotun mai alƙalai uku bayan sauraron koke-koke, ta bayar da umarnin janye takardar shaidar cin zabe da INEC ta ba Yusuf tare da bayar da umarnin a ba Gawuna takardar shaidar cin zabe
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya rusuna ya godewa Allah, jim kaɗan bayan hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaben gwamnan Kano ta yanke na ba ɗan takarar gwamna, Nasir Yusuf Gawuna, nasara.
Bidiyon yadda Ganduje, Gawuna suka yi murna
"Akwai Kura-Kurai": Gwamna Abba Ya Magantu Kan Hukuncin Kotu, Ya Bayyana Mataki Na Gaba Da Zai Dauka
Kotun ta bayyana Nasir Yusuf Gawuna a matsayin zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano tare da tsige Abba Yusuf na jam'iyyar NNPP.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Ganduje da Gawuna cikin murna da jindaɗi bayan kotun ta ayyana jam’iyyarsu a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan jihar Kano da aka yi a ranar 18 ga Maris.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nasiru Yusuf Gawuna ya kasance mataimakin Ganduje na tsawon shekaru hudu a jihar Kano.
Bidiyon yadda Ganduje da Gawuna suka nuna farin cikin su game da hukuncin kotun wanda hadimin Shugaba Tinubu kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun, ya sanya a shafinsa na X (wacce a baya aka fi sani da Twitter), ya jawo kace-nace.
Ƴan Najeriya sun yi martani kan bidiyon Ganduje da Gawuna
Ƴan Najeriya kamar yadda suka saba sun garzaya sashin sharhi na X kuma sun mayar da martani kan yadda Ganduje ya yi murnar nasarar Gawuna a kotu.
@alefreewayy ya rubuta:
"Yi tunanin daga ba ku muƙami kuma an kori shugabanku.. ba wani abu da ya kai wannan ciwo."
@iAbdullaah ya rubuta:
"Ganduje mai zamani."
@Abdullahiabba_ ya rubuta:
"Mun iso."
@KIfarende ya rubuta:
"Lauyoyin da suke nasara a kotun zaɓe ba sa hayaniya, kuma wannan ita ce halayyar lauyoyin da suka san abin da suke yi. Babu hayaniya, babu kafafen sada zumunta, babu wasan kwaikwayo, babu hidimar godiya a coci, kuma babu cin zarafi, ba kamar maƙwabtanmu ba."
Gwamna Abba Zai Garzaya Kotu
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar ta yanke na tsige shi.
Gwamnan ya bayyana cewa akwai kura-kurai a hukuncin kotun, inda ya tabbatar da cewa zai ɗaukaka ƙara domin dawo da nasararsa da ya samu a zaɓe.
Asali: Legit.ng