Tsaffin Gwamnoni Da Wasu Kungiyoyi Na Shirin Tsige Akpabio Daga Shugabancin Majalisar Dattawa

Tsaffin Gwamnoni Da Wasu Kungiyoyi Na Shirin Tsige Akpabio Daga Shugabancin Majalisar Dattawa

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Obot Akapbio na cikin matsin lamba saboda watakila ya rasa mukaminsa na shugabanci majalisar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu tsofaffin gwamnonin da yanzu haka sanatoci ne a majalisar, su ne suke shirin tsige shi
  • Hakazalika, gamayyar ƙungiyar Coalition for Parliamentary Democracy (CPD) ita ma tayi kira da a tsige shi saboda gazawarsa wajen samun biyayya daga ƴan majalisar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Aƙalla tsofaffin gwamnoni 10 ne a majalisar dattawa da gamayyyar wasu ƙungiyoyi ne ke ƙara ƙaimin tsige Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa.

An tattaro cewa wasu na hannun Akpabio a majalisar dattawa sun yi yunkurin shigar da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), Dr. Abdullahi Umar Ganduje, cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

Shirin tsige Akpabio na kara karfi
An taso Akpabio gaba domin ganin an tsige shi Hoto: Godswill Obo Akpabio
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wani jami’in jam’iyyar ya bayyana cewa shugabannin jam'iyyar ba su da masaniya kan halin da Akpabio yake ciki.

"Jam’iyya tana jin abubuwa da dama, amma mun ji cewa wasu Sanatoci na tunanin haduwa da NWC domin su taimaka wajen warware matsalar." A cewarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

CPD ta yi kira da a tsige Akpabio

A halin da ake ciki, gamayyar ƙungiyar Coalition for Parliamentary Democracy (CPD) na kara matsa lamba ga Akpabio da ya sauka daga muƙamin shugabancin majalisar dattawa, cewar rahoton Tribune.

Hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da kodinetan CPD na kasa, Dr. Menike Johnson, ya fitar a ranar Talata, 19 ga watan Satumba.

Johnson ya bayyana cewa gazawar Akpabio wajen gudanar da shugabanci yadda ya dace da kasa samar da sahihin jagoranci na gaskiya shi ne dalilin da yasa suka yanke shawarar neman a tsige shi.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

Sun bayyana shugabancin Akpabio a majalisar dattijai a matsayin wanda ya suma, ya rasa inganci kuma ba zai iya samun biyayya daga ƴan majalisar ba.

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar Bulkachuwa

A wani labarin kuma, babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja, ta zartar da hukuncinta kan ƙarar da tsohon Sanatan Bauchi ta Arewa ya shigar yana neman a hana hukumar ICPC bincikensa.

Alƙalin kotun mai shari'a Inyang Ekwo, ya yi fatali da ƙarar inda ya bayyana cewa ba ta da inganci ko kaɗan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng