Jami'an Yan Sanda Sun Cafke Yan Ta'adda 5 a Jihar Benue

Jami'an Yan Sanda Sun Cafke Yan Ta'adda 5 a Jihar Benue

  • Jami'an ƴan sanda a jihar Benue sun samu nasarar cafke wasu gawurtattun ƴan ta'dda da suka addabi al'ummar jihar
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ta bayyana cewa jami'in tsaro na musamman ne suka jagoranci cafko miyagun
  • A cewarta ƴan ta'addan mutum biyar ne suka shigo hannu bayan jami'an tsaron sun ritsa su a cikin daji

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Benue - Rundunar ƴan sandan jihar Benue ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci da garkuwa da mutane a yankin Sankera na jihar.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Catherine Anene, a cikin wata sanarwa ta ce an cafke waɗanda ake zargin ne a ƙoƙarin da jami'an tsaro ke yi na kawo ƙarshen ayyukan ta'addanci a yankin, cewar rahoton Daily Trust.

Yan sanda sun cafke yan ta'adda a jihar Benue
Mukaddashin babban sufetan yan sanda na kasa, Kayode Adegbotokun Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A cewar kakakin jami'an tsaro na atisayen Zenda JTF ne suka bi sawun ƴan ta'addan sannan suka cafke su.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Jihar Arewa, Sun Sace Mahaifi Tare Da Diyarsa

Yadda ƴan sanda suka cafke ƴan ta'addan

Sanarwar na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A ci gaba da murƙushe ƴan bindiga da ayyukansu a yankin Sankera na jihar Benue, jami'an ƴan sanda na atisayen Zenda JTF sun bi sawu tare da cafke wasu ƴan ta’adda waɗanda ke ƙarƙashin jagorancin Anyogor Mnguor da Terhemen Mzaga, wanda aka fi sani da Fullfire."
"Waɗannan ƴan ta'addan sun ƙware wajen yin garkuwa da mutane da kai hare-hare da kisan jama’a. Na baya-bayan nan shi ne kisan gillar da aka yi wa mutanen Akpuna a ranar 21/7/2023 a ƙaramar hukumar Ukum."
"A yayin aikin, waɗanda ake zargin da aka cafke sun haɗa da Ordoonku Sunday Kusuv, Msughter Nyieyem, Terkaa Tayough da Liambee Adeadegh, wanda aka fi sani da Don-Konyo. An ƙwato harsasai guda tara daga hannunsu."
"Hakazalika an cafke wani Sonter Felix Tyozughul da laifin yin garkuwa da Dr. Asema Msuega, likita a babban asibitin Ukum, a ranar 23/07/2023, wanda tuni aka sake shi. Wanda ake zargin ya amsa cewa da hannunsa dumu-dumu a aikata laifin."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji da 'Yan Sanda Da Dama a Jihar APC

Yan Bindiga Sun Sace Manomi Da Diyarsa

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun yi awon gaba da wani mahaifi tare da ɗiyarsa a jihar Kwara.

Ƴan bindigan sun ɗauke mutumin ne wanda manomi ne, lokacin da yake dawowa daga gona tare da ɗiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng