Gaskiya Ta Bayyana Kan Ikirarin Dele Momodu Na INEC Ta Kashe N355bn Kan BVAS

Gaskiya Ta Bayyana Kan Ikirarin Dele Momodu Na INEC Ta Kashe N355bn Kan BVAS

  • Ikirarin da Dele Momodu, ɗan takara a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya yi, na cewa INEC ta kashe N355bn akan BVAS ba gaskiya ba ne
  • Wani bincike da aka yi kan kasafin kuɗin INEC a zaben 2023 ya nuna hukumar zabe ta kashe N117.1bn kan kayayyakin fasahar zabe
  • Na'urar BVAS ta faɗo a ƙarƙashin N117.1bn na kudin fasahar zabe, wanda ya saɓa da iƙirarin da Dele Momodu ya yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi ikirarin cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), a zaben 2023, ta kashe naira biliyan 355 kan na'urar BVAS.

A cewar TheCable, mawallafin na mujallar Ovation ya yi wannan iƙirarin ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Instagram a ranar Talata, 19 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

Dele Momodu ya yi ikirarin INEC ta kashe N355bn kan BVAS
An yi binciken gaskiya kan ikirarin Dele Momodu Hoto: Dele Momodu
Asali: Twitter

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"Me yasa muke ɓarnatar da albarkatunmu marasa yawa yayin da za mu iya canza dimokuradiyya zuwa sarauta."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"N355 biliyan domin BVAS, kuma mutane biyar sun ce ba dole ba ne a yi amfani da ita? Wannan ba abin dariya ba ne? Wannan wacce irin ƙasa ce?"
Dele Momodu ya yi ikirarin INEC ta kashe N355bn kan na'urar BVAS
Dele Momodu ya zargi INEC da kashe N355bn kan BVAS Hoto: Dele Momodu
Asali: Twitter

Haƙiƙanin kuɗin da aka kashe a kan BVAS

A lokacin da yake kare kasafin kuɗin hukumar a gaban kwamitin majalisar dattawa kan kasafin kuɗi, shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Mahmud Yakubu ya bayyana cewa hukumar zabe za ta kashe naira biliyan 305 domin gudanar da babban zabe na 2023.

Yakubu a bayaninsa ya bayyana cewa Naira biliyan 50 ne aka ƙiyasta a matsayin kasafin kudin hukumar na 2023 yayin da aka ware Naira biliyan 305 domin gudanar da babban zaɓe.

Kara karanta wannan

Bashin Da Ake Bin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan 87, An Fadi Abinda Kowane Dan Ƙasa Zai Biya

Shugaban hukumar ya cigaba da cewa, hukumar ta ƙiyasa N161.9bn na ayyukan gudanar da zabe da kuma kuɗaɗen gudanarwa, N117.1bn na kuɗin kayayyakin fasahar zaɓe, N18.5bn na kuɗin zaɓe.

Don haka, kasafin kudin na'urar BVAS ya fadi ne a karkashin kudin kayayyakin fasaha, wanda ya kai Naira biliyan 117.1.

Bayanan da aka gabatar sun ci karo da iƙirarin jigon PDP, Dele Momodu.

INEC Ta Amince Da Kafa Sabuwar Jam'iyya

A wani labarin kuma, hukumar zaɓe mai zaman kanta ts ƙasa ta amince da kafa wata sabuwar jam'iyya a ƙasar nan.

Kwamishinan INEC na ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da ilimantar da masu kaɗa kuri'a, Festus Okoye, ne ya bayyana haka a wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng