Babban Jigo a Jam'iyyar Peter Obi Ta Labour Party Ya Rasu
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi rashin ɗaya ɗaga cikin manyan magoya bayansa
- Peter Obi ya aike da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar ɗan a mutun nasa wanda ya kafa ƙungiyar magoyan Peter Obi ta ƙasa, Churchill Enyia
- Obi ya bayyana rasuwar Enyia a matsayin wani babban rashi ga iyalansa, jam'iyyar Labour Party da magoya bayanta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Onitsha, jihar Anambra - Churchill Enyia, wanda ya kafa ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta ƙasa ya rasu.
Legit.ng ta rahoto cewa Marigayi Enyia kwararre ne kan hulɗa da jama’a kuma wanda ya ƙware wajen tattaro mutane.
Obi ya yi ta'aziyyar wani fitaccen mai goyon bayansa, Churchill Enyia
Ko da yake cikakkun bayanai game da mutuwarsa ba su gama fitowa ba, marigayin ya yi bankwana da duniya ne a cikin wannan satin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake aikewa da saƙon ta'aziyyarsa kan mutuwar Enyia, Obi a wani rubutu a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 19 ga Satumba, ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi.
A kalamansa:
"A madadin iyalaina, jam’iyyar Labour Party, da ƴan Obidient, ina miƙa ta’aziyya ga iyalan Amb. Churchill Enyia, jagora mai hangen nesa wanda ya kafa ƙungiyar magoya bayan Peter Obi ta kasa."
"Ya taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ƴan Najeriya a lokacin yaƙin neman zaɓenmu kuma ya ba da gudummawar da ba za a iya kwatantawa ba ga manufarmu ta kafa sabuwar Najeriya."
"Ina roƙon Allah wanda ya mayar da shi zuwa gidansa na gaskiya a wannan lokaci, ya ba shi hutawa ta har abada, ya kuma baiwa iyalansa da ƴan Obidient, da dukkaninmu baki ɗaya ikon haƙuri da jure wannan babban rashin da muka yi."
Dan Majalisa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga jimami bayan wani ɗan majalisa mai ci a jihar Rivers, ya yi bankwana da duniya.
Dinebari Loolo wanda kafin rasuwar shi ya wakilci mazabar Khana 2 da ke karamar hukumar Khana a majalisar jihar ya rasu ya bar iyalai da dama.
Asali: Legit.ng