Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203

Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203

An gudanar da jana’izar Alhaji Mohammed Abubakar Bello da aka fi sani da suna Baba Masaba wanda ya auri mata sama da dari a garin a ranar Lahadi 29 ga watan Janairu inda aka binne shi a garin Bidda.

Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203
Baba Masaba

Babban limami Alh Mohammed Baba Kutigi ne ya ja sallar, inda aka jiyo muryoyin mutane suna ta kabarbari.

KU KARANTA:Kwana sun kare: Mai mata 97 ya kwanta dama

A ranar Asabar ne Baba Masaba ya rasu bayan jinyar wata gajeruwar rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 93. A shekarar 2008 ne Masaba ya shaida ma Duniya cewar yana da mata 83 da yaya 107.

Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203
Baba Masaba ya mutu ya bar mata 130 da ýaýa 203

Amma wakilin jaridar Saily Trust ya binciko cewar zuwa ranar da Masaba ya rasu, matayensa sun kai 130. Sa’annan ya mutu ya bar yaya 203, da jikoki rutu rutu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel