Ministan Makamashi Adebayo Adelabu Ya Alwashin Samar Da 20,000MW Na Wutar Lantarki

Ministan Makamashi Adebayo Adelabu Ya Alwashin Samar Da 20,000MW Na Wutar Lantarki

  • Ministan makamashi da gaske yake wajen ganin ƙasar nan na samar da wadatacciyar wutar lantarki
  • Adebayo Adelabu ya sha alwashin nan da shekara uku masu zuwa zai samar da 20,000MW na wutar lantarki a ƙasar nan
  • Adebayo ya bayyana ya yi bincike sosai kan matsalar rashin wutar inda ya nuna hanyoyin magance matsalolin ba masu wuya ba ne

Jihar Legas - Adebayo Adelabu, ministan da Shugaba Tinubu ya ba ragamar ma'aikatar makamashi, ya sha alwashi a madadin gwamnatin tarayya na samar da 20,000MW na wutar lantarki.

Ministan ya bayyana cewa zai samar da wannan adadin ne a cikin shekaru uku masu zuwa, cewar rahoton Leadership.

Ministan makamashi zai samar da 20,000MW
Adelabu ya sha alwashin samar da 20,000MW na wutar lantarki Hoto: Adebayo Adelabu
Asali: Facebook

Duk da cewa ƙasar ta gaza samar da abin da ya wuce 4,000MW na wutar lantarki, Adelabu ya haƙiƙance cewa gwamnatin Shugaba Tinubu za ta cimma samar da 20,000MW na wutar lantarki nan da shekarar 2026.

Kara karanta wannan

Manyan Hadiman Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Ƙara Yi Wa PDP Babban Lahani, Sun Koma APC

Adelabu ya gama gano matsalolin lantarki a Najeriya

Adelabu, wanda ya yi magana a wajen taron makamashi na Najeriya na bana a Legas, ya bayyana cewa ya yi binciki mai zurfi kan matsalolin inda ya gano cewa mafita ba ta da wahala kamar yadda mutane suke tsammani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A kalamansa:

"A matsayina na ɗan siyasa, ministan makamashi, ina da ɗan ƙanƙanin lokaci akan mulki, kuma dole ne in yi tasiri. Na kuduri aniyar yin tasiri. Na yi bincike mai zurfi kan matsalar kuma na gano cewa mafitar ba ta da wahala kamar yadda muka yi amanna."
"A wajen sanya abubuwan da mu ke son cimmawa, muna buƙatar sanya masu ɗan gajeran zango. Burina shi ne mu ƙara yawan wutar lantarkin da muke adanawa zuwa aƙalla 20,000MW a cikin shekara uku masu zuwa. Ba a iya nan kawai za mu tsaya ba."

Kara karanta wannan

Magana Ta Fito: Na Kusa da Atiku Abubakar Ya Tona Asirin Gwamnatin Shugaba Tinubu Kan Abu 1 Tal

"Za mu iya fitar da kaso 80 na daga cikin wutar lantarkin da aka adana ga mutane waɗanda za su iya amfani da ita."

FG Ta Kara Farashin Mitar Wutar Lantarki

A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar sa ido kan wutar lantarki a Najeriya (NERDC) ta ƙara farashin mitar wutar lantarki a faɗin ƙasa.

Mitar wutar da ake badawa a baya a kan naira 58,661.69, yanzu za ta koma naira 81,975.16, yayin da babbar wannan da ake badawa akan naira 109,684.36, yanzu za ta koma naira 143,836.10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng