Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Ba Sarakuna Hakuri
- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana wata Taiwo Obasanjo wacce ta yi ikirarin ita matarsa ce tare da ba da hakuri a madadinsa a matsayin sojar gona
- Wata sanarwa daga ofishin tsohon shugaban kasar ta ce Taiwo Obasanjo ta dai haifa ma Obasanjo yara biyu ne, amma ba matarsa bace
- A cewar sanarwar, babu wanda ya isa ya yi magana da yawun iyalan Obasanjo sai wadanda aka ba izinin yin hakan
Abeokuta, Ogun - Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya, ya karyata wata Taiwo Obasanjo, wacce ta yi ikirarin cewa ita matar tsohon janar din ce tare da bayar da hakuri a madadinsa kan abun da ya yi wa sarakunan Yarbawa a jihar Oyo.
PM News ta rahoto cewa sojar gonar ta yi kira ga sarakunan da su yafewa tsohon shugaban kasar kan sawa da ya yi suka tashi tsaye da zama kamar wasu yaran makarantar firamare a wajen wani taro a jihar Oyo.
Matar Obasanjo ta ba da hakuri a madadin tsohon shugaban kasar
A wani jawabin neman yafiya, Misis Taiwo ta bukaci yan Najeriya da mutanen duniya da su yafewa mijinta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai dai kuma a ranar Litinin, 18 ga watan Satumba, tsohon shugaban kasar ya ce an ja hankalinsa zuwa ga wata sanarwa daga matarsa, yana mai cewa an hada hotonsa ne da na wata Misis Taiwo Martins, marubuciyar sanarwar.
Tsohon shugaban kasar ya ce:
"Don fayyace gaskiya, Ms Martins ta haifawa Obasanjo yara biyu, Jonwo da Bunmi, amma dai ba matarsa bace ko kuma wata dangin iyalin Obasanjo."
Obasanjo ya ce tsohuwar matarsa sojar gona ce
Sanarwa daga ofishin tsohon shugaban kasar ta jaddada cewa ikirarin Taiwo na cewa ita matar Obasanjo ce ba gaskiya bane kuma ana iya daukar ta a matsayin sojar gona.
Ya kara da cewar babu wanda ke da ikon yin jawabi a madadin iyalin Obasanjo sai dai tsohon shugaban kasar da kansa ko wadanda aka daurawa alhakin yin haka a hukumance.
Kehinde Akinyemi, mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Obasanjo ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Litinin.
Matar Obasanjo ta ba sarakuna hakuri a madadinsa
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Taiwo Obasanjo, uwargidan tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, ta roƙi afuwa a madadin mijinta, wanda ya umarci sarakunan Yarbawa da su tashi tsaye yayin wani taro a Iseyin, jihar Oyo a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba.
Taiwo Obasanjo ta miƙa rokonta ga ɗaukacin Yarabawa na duniya, inda ta roƙi samun yafiya ta dindindin mai ɗorewa.
Asali: Legit.ng