Mutum 5 Sun Rasa Ransu a Wani Hatsarin Mota Kan Titin Lagos-Ibadan
- Wsni hatsarin mota da ya auku akan titin hanyar Legas-Ibadan ya salwantar da rayukan fasinjohi biyar da raunata
- Hatsarin wnada ya auku a safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Satumba, ya faru ne a dalilin fashewar taya da kuma gudun da ya wuce ƙa'ida
- Wasu fasinjojin sun ssmi raunika inda aka garzaya da su asibiti domin ba su cikakkiyar kulawar da ta dace
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Aƙalla mutane biyar ne aka tabbatar sun rasa ransu bayan da wata mota ƙirar bas da wata motar ɗaukar kaya suka afkawa wata babbar mota a kusa da sansanin Foursquare da ke kan titim hanyar Legas zuwa Ibadan.
Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa, kakakin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a Ogun, Florence Okpe, ta tabbatar da aukuwar lamarin yayin wata tattaunawa da manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar.
Okpe ta bayyana cewa hatsarin ya auku a ranar Lahadi, 17 ga watan Satumban 2023, da misalin ƙarfe 6:15 na safe, rahoton Channels tv ya tabbatar.
Yadda hatsarin ya auku
Ta ce motar ta faɗi ne bayan da tayoyin ta suka fashe saboda tsananin gudu wanda hakan ya haifar da hadarurruka da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce mutane 21 ne hatsarin ya ritsa da su, inda ta ƙara da cewa fasinjoji biyar sun mutu, yayin da wasu 12 suka samu raunuka.
Kakakin ya ce an garzaya da fasinjojin da suka jikkata zuwa asibitin Victory Hospital da ke a Ogere, kusa da Abeokuta.
An kuma ajiye gawarwakin fasinjojin da suka rasa rayukansu a dakin ajiye gawa da ke ƙauyen Ipara kusa da Abeokuta.
Kakakin ta ƙara da cewa, Anthony Uga, kwamandan hukumar FRSC a Ogun, ya bukaci masu ababen hawa da su guji amfani da tayoyin da ba su da inganci a cikin motocinsu, su kuma yi taka tsantsan wajen yin tuƙi yayin da ake yin ruwan sama.
Rayukan Mata 5 Sun Salwanta
A wani labarin kuma, Wani mummunan hatsari ya rutsa da motar bas ta haya kirar L300 da kuma babbar motar dakon kaya 'Leyland' a mahadar Odumudu da ke kan babban titin Nteje-Awka, jihar Anambra.
Hatsarin ya lakume rayukan fasinjoji biyar yayin da wasu biyar kuma suka samu raunuka daban-daban.
Asali: Legit.ng