Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida

Uwargidar gwamnan jihar Kwara, Misis Olufolake Abdulrazaq, ta hayar muhalli ga Risikat, mace mai launin ido tamkar na mage, wacce aka sake daura auranta da mijinta da ya guje ta, Abdulwasiu Omodada.

Sakataren labarai na uwargidar gwamnan, Yinka Adeniyi, ya ce Olufolake, ta shirinta mai zaman kansa, Ajike Support Group, ta sama wa ma’auratan muhalli mai dakuna biyu a birnin Ilorin.

Adeniyi ya fada ma jaridar Punch a ranar Litinin cewa, an mika wa ma’auratan makulin gidan wanda aka yi masu hayarsa a ranar Juma’a.

Ya ce an karbi gidan ne a yankin da suke ra’ayi a garin Ilorin.

Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida
Mace mai idon mage: Uwargidar gwamna ta karbarwa ma’auratan hayar katafaren gida Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

Adeniyi, wanda ya ce akwai wasu tsare-tsare da uwargidar gwamnan ta shirya wa matar da mijinta, ya bayyana cewa: “Mun so sama wa matar shago domin siyar da magunguna, amma sai muka biya kudin shagon da na gidan, an sanar da mu cewa wani ya riga ya biya kudin shagon don haka muka umurci ma’auratan da su nemo wani shagon.

“Daga bisani gidauniyar Ajike za ta sama wa matar lasisin aiki a matsayin mai siyar da magunguna sannan a zuba mata kayayyaki a shagon.”

A halin da ake ciki, sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya shawarci Risikat da Abdulwasiu da su zauna lafiya sannan su yi hakuri da junansu a gidan auransu.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta kashe yan ta’adda 9, sun ceto mutum 7 a Gwoza

Sulu-Gambari ya bayar da shawarar ne a ranar Asabar a wajen daurin auren su a masallacin Ajijola Anabi, Ayegbami, yankin Okelele na Ilorin.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Sarkin Kakakin Ilorin, Alhaji Abdulwasiu Gafar, ya shawarci ma’auratan da su zauna cikin aminci daga yanzu.

A wa’azinsa, limamin masallacin, Alhaji Jamiu Ajijola-Anabi, ya bukaci ma’auratan da su zauna cikin kauna da aminci da wadatar zuci.

KU KARANTA KUMA: Kada ku koma ajujuwa idan aka bude makarantu, NUT ga malamai

A baya mun kawo maku cewa an sake kulla aure tsakanin matar nan mai ido launin na mage, Risikat Azeez da tsohon mijinta daya gujeta, Wasiu Omo-Dada.

Bikin ya samu halartan yan uwa da abokan arziki a gidan Alfa Ajijola-Anabi, Aiyegbami, a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba.

Risikat ta yi fice a watan Agusta bayan wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa labarinta a yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel