An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)

An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)

- An sasanta tsakanin matar nan mai ido launin shudi irin na mage, Risikat Azeez da mijinta wanda ya watsar da su

- An gano hotunan ma’auratan tare yayinda ake sake daura masu aure a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara

- Matar da yaranta sun samu tallafi daga yan Najeriya bayan mijinta ya gudu ya barsu saboda launin idanunsu me kama da na mage

Daga karshe dai an sake kulla aure tsakanin matar nan mai ido launin na mage, Risikat Azeez da tsohon mijinta daya gujeta, Wasiu Omo-Dada.

Bikin ya samu halartan yan uwa da abokan arziki a gidan Alfa Ajijola-Anabi, Aiyegbami, a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba.

Risikat ta yi fice a watan Agusta bayan wani mai amfani da shafin Twitter ya wallafa labarinta a yanar gizo.

An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)
An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

A wata hira da ita, Risikat ta bayyana cewa mijinta ya tafi ya barta da yaranta mata su biyu saboda launin idanunsu da ya kasance tamkar na mage.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gidaje, shaguna sun kone kurmus yayinda motar tanka ta kama da wuta a jihar Neja

Sai dai mijin a wata hira ta daban ya karyata cewar ya yi watsi dasu saboda launin idanunsu.

A karshe dai sun daidaita, har suka yi hotuna cikin so da kauna, sannan aka sake daura masu aure a ranar Asabar da ya gabata.

An gano hotunan ma’auratan tare yayinda ake sake daura masu aure a Ilorin, babbar birnin jihar Kwara.

Matar da yaranta sun samu tallafi daban-daban daga yan Najeriya tun bayan da labarinta ya bayyana a yanar gizo, sannan idon nasu ya zamo abun sha’awa a tsakanin mutane da ke musu kallon yan baiwa.

Ga karin hotunan bikin a kasa:

An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)
An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)
An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta (Hotuna)
An sake daura auren 'mace mai idon mage' da tsohon mijinta da ya gujeta Hoto: Linda Ikeji
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun halaka wani hazikin sojan sama a Kaduna (hoto)

A gefe guda, mun ji cewa an sha shagalin wani mutum wanda ake cewa yafi kowa muni a duniya.

Godfrey Baguma mai wasan bada dariya ne a kasar Uganda, kuma an fi saninsa da Ssebabi.

Mafi munin mutumin a fadin duniyar ya aura masoyiyarsa a matsayin mata ta uku a wani irin kasaitaccen biki mai cike da shagali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel