Kano: Abba Gida Gida Ya Gargadi Kan Kara Kudin Makarantu Da Sayen Litattafai
- Gwamnatin Kano ta yi kakkausan gargadi ga makarantu masu zaman kansu a fadin jihar
- Mai ba gwamna shawara ta musamman kan makarantun masu zaman kansu, Baba Umar, ya ce daga yanzu ba a yarda wata makaranta ta kara kudin makaranta ba bisa ka'ida ba
- Gwamnatin Abba Gida Gida ta kuma hana makarantu masu zaman kansu tilastawa iyaye siyan litattafai da inifam a cikin makaranta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Mai ba gwamnan jihar Kano shawara ta musamman kan makarantun masu zaman kansu, Baba Umar, ya gargadi mamallakan makarantu masu zaman kansa wadanda ke cajin kudin makaranta da yawa ba bisa ka'ida ba da su daina.
Ya ce gwamnatin jihar Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ba za ta nade hannayenta ta bari a ciki gaba da irin wannan abu ba.
Baba Umar wanda ya yi gargadin yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kano a ranar Juma'a, 15 ga watan Satumba, ya ce daga yanzu babu wani mai makaranta da aka ba damar kara kudin makaranta ba tare da ya bi ka'idojin da aka shimfida ba.
Kada makarantar da ta tilasta iyaye siyan litattakai da inifam daga wajenta, gwamnatin Kano
Haka kuma ya ce daga yanzu babu masu makarantar da ke da damar tilasta iyaye siyana litattafai da inifam daga makarantunsu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, duk masu yin kakkausar suka ga gwamnati kan matakan da ake dauka don duba abubuwan da shugabannin makarantu ke yi , suna yin hakan ne domin kare ayyukansu da suka sabawa doka.
Hadimin gwamnan ya ci gaba da cewa, duk shugaban makarantar da bai gamsu da matakan da gwamnati ta dauka don tsaftace tsarin ba, toh ya nemi a yi shari;a.
Za a janye lasisin makarantu masu zaman kansu da basu dawo da fom din da suka cika ba
Gwamnatin ta kuma yi barazanar janye lasisin duk mai makaranta mai zaman kansa da ya ki cikawa da mayar da takardar da aka sabunta musu kwanan nan.
Ya ce bayar da fom ga masu makarantun ya zama dole don bai wa gwamnati damar samun bayanan dalibai a duk makarantu masu zaman kansu.
Umar ya ce a cikin makarantu sama da 7,000 da ake da su a Kano, 2,000 ne ya zuwa yanzu suka cika suka mika fom dinsu.
Ya bayyana cewa makarantun masu zaman kansu suna ta saba ka’idojin da aka gindaya wadanda suka hada da biyan harajin kashi 10 na kudaden makarantar da suke karba.
Umar ya ce:
"Mun gano cewa yawancin masu makarantun a maimakon biyan harajin su a asusun gwamnati, suna karkatar da shi zuwa wasu asusu na kashin kai tsohon babban sakataren hukumar."
A Kokarin Gyara A Harkar Ilimi, Abba Kabir Ya Dauki Mummunan Mataki Kan Wasu Shugabannin Makarantu 2 A Kano
Abba gida gida ya sallami kwamishinan da ya yi barazana ga alkalan kotun zabe
A wani labarin, mun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kori kwamishinan Safiyo a jihar, Adamu Aliyu daga mukaminsa.
Gwamnan ya dauki wannan matakin ne kan kalaman kwamishinan a jiya inda ya ke barazana ga alkalan kotun zabe.
Asali: Legit.ng