Tinubu Ya Nada Yaron El-Rufai Mukamin Mataimakin Gwawnan Babban Bankin CBN
- A wani yanayi na fara saka wa El-Rufai, Shugaba Tinubu ya nada yaron tsohon gwamnan Kaduna babban mukami
- Tinubu ya nada tsohon kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Muhammad Sani Dattijo mataimakin gwamnan bankin CBN
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Juma’a 15 ga watan Satumba
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada na hannun daman Nasiru El-Rufai, Muhammad Abdullahi Dattijo a matsayin mataimakin gwamnan babban bankin CBN.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Juma’a 15 ga watan Satumba.
Waye ne Dattijo da Tinubu ya nada a wurin El-Rufai?
Dattijo ya taba rike mukamin kamishinan kasafi da tsare-tsare a lokacin mulkin Nasir El-Rufai, Legit ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A nada Dattijo da wasu mutane uku wadanda su ka hada da Emem Nnana Usoro da Philip Ikeazor da kuma Dakta Bala M Bello.
Rahotanni sun tattaro cewa, Shugaba Tinubu ya umarci korar dukkan mataimakan gwamnan babban bankin na CBN da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada.
Yaushe za a tabbatar da Tinubu ya nadan a majalisar Dattawa?
Kamar yadda sanarwar ta tabbatar, ana tsammanin sabbin wadanda aka nada mukaman da kawo sauyi a tsarin babban bankin kasar.
Har ila yau, ana bukatar su da kara wa 'yan Najeriya kwarin gwiwar ganin an dawo da martabar bankin da kuma inganta tattalin arziki, Daily Trust ta tattaro.
Bayan tabbatar da su a majalisar Dattawa, wadanda aka nadan za su yi aiki har na tsawon shekaru biyar a nan gaba.
Tinubu Ya Nada Sabon Gwamnan CBN da Mataimakansa 4
A wani labarin, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da nadin Dakta Olayemi Michael Cardoso, a matsayin sabon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).
Rahotanni sun tabbatar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada sabon gwamnan CBN na tsawon shekaru 5 da zaran majalisar dattawa ta tabatar ta shi.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bola Tinubu Ajuri Ngelale, ya fitar a yau Jumu'a 15 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng